Xavi na dab da zama kocin Barcelona, in ji Al Sadd

Asalin hoton, Reuters
Tsohon dan wasan Barcelona Xavi ya shirya tsaf domin zama kocin kungiyar, in ji Al Sadd yana mai cewa an amince ya jagoranci kungiyar ta Sifaniya.
A baya dai kungiyar da ke Qatar ta ce ba za ta bari kocin nata mai shekara 41 ya tafi Barca ba.
Xavi, wanda ya buga wasa sau 779 kuma ya ci wa Barca kofuna 25, ya bayyana karara cewa yana fatan "tafiya gida" domin zama kocin Barca kuma za a iya cimma yarjejeniyar hakan.
Kungiyar Al Sadd ta ce Barca ta biya kudin da za su sa ta saki Xavi.
Xavi ya bar Barcelona zuwa Al Sadd a 2015, inda da farko ya soma murza mata leda kuma daga bisani yake horas da 'yan wasanta.
Ya zama kocin kungiyar bayan ya yi ritaya da buga tamaula a 2019 kuma ya jagorance su zuwa gasar lig ta kakar da ta wuce. Sun yi wasan lig 36 ba tare da an doke su ba.
Kungiyar ta Qatar ta wallafa sakon Tuwita da ke cewa Xavi "muhimmin bagare ne na tarihin Al Sadd" kuma ta yi masa fatan alheri kan abin da zai yi nan gaba.

Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da Barcelona ta kori Ronald Koeman ranar 27 ga watan Oktoba ake alakanta Xavi da batun komawa Nou Camp inda ya shafe kurciyarsa a matsayin dn kwallon kafa.











