Lionel Messi ya yi mafarkin cin kofin Champions League a Paris St-Germain

Lionel Messi ya ce ya yi mafarkin lashe Champions League, bayan da ya koma Paris St-Germain, ya kara da cewar "Ina jin muna da 'yan wasan da za mu iya daukar kofin a nan."

Kyaftin din Argentina, mai shekara 34 ya ci Champions League hudu a Barcelona, na karshe da ya dauka a kungiyar shine a 2015.

PSG tana ta kokarin daukar kofin farko a gasar ta Zakarun Turai, bayan da ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Bayern Munich a 2020.

''Buri na da mafarkin da nake yi shine na kara daukar kofin Champions League.'' Kamar yadda Messi ya sanar a lokacin da aka gabatar da shi a matakin dan wasan PSG.

Messi ya bar Barcelona - Kungiyar da ya koma tun yana da shekara 13 - bayan da ta kasa kulla sabuwar yarjejeniya da shi, saboda dokar La Liga ta kashe kudi daidai aljihun kungiya.

Daya daga fitatcen dan wasa a duniya a wannan karnin, ya ci kwallo 672 a wasa 778 da ya yi wa kungiyar Sifaniya.

Ya lashe kyautar Ballon d'Or karo shida da cin kofi 35 a Nou Camp, ya kuma ce ''Ina murna da zan buge wani sabon shafin rayuwa a fannin taka leda'' bayan ''mawuyacin halin'' da na bar Barcelona.

Messi ya saka hannun kan yarjejeniyar kaka biyu da sharadin za a iya tsawaitata kaka daya idan ya taka rawar gani a Paris St Germain.

A kokarin da PSG ke yi na ganin ta lashe kofin Zakarun Turai, kungiyar ta dauki wadanda suka dauki Champions League da suka hada da Sergio Ramos da Georginio Wijnaldum da kuma Messi.