Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Gueye, Herrera, Ederson, Martial, Lukaku,
Paris St-Germain za ta sayar da manyan 'yan wasanta kusan goma domin ta samu kudin cike gibin da ta samu sakamakon sayen kyaftin din Argentina Lionel Messi, mai shekara 34.
Dan wasan tsakiya na Senegal Idrissa Gueye, mai shekara 31 da na Sifaniya Ander Herrera, shi ma mai shekara 31da kuma dan Argentina Mauro Icardi mai shekara 28 na daga cikin wadanda za ta sayar. (Jaridar Sport ta Sifaniya)
Manchester City na shirin fara sabuwar tattaunawa da golanta dan Brazil Ederson, mai shekara 27 da kuma dan wasan tsakiya na Ingila Phil Foden, mai shekara 21, kan sabon kwantiragi a kungiyar. (Mail)
Manchester United ba ta da niyyar sayar da Anthony Martial a bazaran nan, bayan da ake danganta dan gaban na Faransa mai shekara 25 da tafiya Inter Milan. (Jaridar Telegraph)
Har yanzu Tottenham na tattaunawa don sayen Lautaro Martinez, mai shekara 23, duk da rahotannin da ke nuna cewa Inter Milan ba ta da niyyar sayar da dan wasan na Argentina tare da kuma Romelu Lukaku mai shekara 28, wanda shi tuni yana kamala shirye-shiryen komawarsa Chelsea. (Football Insider)
Arsenal da Tottenham da kuma Everton na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Switzerland Denis Zakaria, mai shekara 24, daga Borussia Monchengladbach. (jaridar Bild ta Jamus)
An samu tazara sosai a cinikin dan wasan Liverpool Xherdan Shaqiri inda kungiyar ta ke son Lyon wadda ke son dan gaban na Switzerland mai shekara 29 ta biya akalla fam miliyan 12. (Liverpool Echo)
Everton na shirin taya dan bayan kungiyar Antwerp, dan Portugal Aurelio Buta, mai shekara 24, wanda Celtic ma ke so, fam miliyan 3. (Jaridar Sun)
Arsenal na son ci gaba da rike dan bayanta Rob Holding, mai shekara 25, duk da rahotannin da ke cewa Newcastle da Leicester na son dan Ingilar. (Football.London)
Dan gaban Everton Richarlison, mai shekara 24, ka iya taka wa kungiyar leda a wasanta na farko na gasar Premier da Southampton, ranar Asabar, duk da rashin hutun bazara da bai yi ba, bayan wasannin gasar cin kofin kasashen Latin Amurka da kuma na gasar Olympic da ya yi wa Brazil a Tokyo. (Liverpool Echo)
Chelsea ta kafe lalle sai fam miliyan 25 za ta sayar da dan bayanta, dan Faransa Kurt Zouma, mai shekara 26, wanda West Ham ke so. (90 Min)
Darektan kwallon kafa na Sevilla Monchi na jiran Chelsea ta kirawo shi, kafin ya fara kokarin dauko wa kungiyar dan bayan Faransa Jules Kounde mai shekara 22. (Express)
Arsenal na jiran Martin Odegaard ya yanke shawara a kan matsayinsa da Real Madrid kafin ta fara kokarin sayen dan wasan na tsakiya, dan Norway mai shekara 22 ya zauna dindindin a Emirates. (DefensaCentral, ta jaridar Express)