Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lionel Messi: Ko Barcelona za ta jingine riga mai lamba 10 da kyaftin din Argentina ya sa?
Ranar Alhamis Lionel Messi ya bar Barcelona, kungiyar da ya yi kaka 21 yana buga wa tamaula.
Tuni dan wasan mai shekara 34 ya yi ban kwana da kungiyar da kuma 'yan wasa ranar Lahadi da kawo yanzu ya kulla yarjejeniya da Paris St Germain.
Ranar Lahadi 15 ga watan Agusta Barcelona za ta fara wasan farko a La Liga kakar 2021-22 ba tare da Messi ba da riga mai lamba goma.
Kungiyar ta yi wasa ranar Lahadi a karon farko ba tare da dan kwallon Argentina ba, inda ta doke Juventus da ci 3-0.
A karawar Sergio Busquets ne ya yi kyaftin koda yake ba dan wasan da ya sa riga mai lamba 10 a ranar.
Messi ya fara sa riga mai lamba 10 a Barcelona cikin shekarar 2008 zuwa 2021, wanda rigar na kasa kawo yanzu.
Ba kasafai ake jingine riga ba a Sifaniya duk kwazon da dan wasa zai yi a tamuala kamar yadda ake yi a gasar Serie A da Roma ta jingine rigar Toti.
A Premier League ma Chelsea ta ajiye riga mai lamba 25 da Gianfranco Zola ya yi amfani da ita, da kuma yadda ake yi a gasar kwallon kwandon Amurka.
A fannin kwallon kafa riga mai lamba 10 tana da daraja, ana bai wa fitattun 'yan wasa da suka kware wajen taka leda da bajinta.
Duk tawagar kwallon kafa ko kungiya kan auna kwazon dan wasa kafin ta bashi riga mai lamba 10, kuma duk wanda ya sa za kaga yana da kwazo ko yaya yake.
Fitattun 'yan wasa da suka sa riga mai lamba 10 a Barcelona suka yi suna a duniya sun hada da Romario da Ronaldinho da Diego Maradona da Rivaldo da kuma Messi.
Jerin wadanda Barcelona ta bai wa riga mai lamba 10 tun da aka kirkiro sa lamba a rigar tamauala:
- Angel Cuellar (1995-1996)
- Giovanni (1996-1997)
- Jari Litmanen (1999-2000)
- Rivaldo (2000-2002)
- Juan Roman Riquelme (2002-2003)
- Ronaldinho (2003-2008)
- Lionel Messi (2008-2021)