Lionel Messi: Shin La liga ta zama lami bayan rasa fitattun ƴan ƙwallon duniya?

Babu Lionel Messi ba Cristiano Ronaldo - Yaya La liga da hamayyar Clasico za ta kasance ?

Hankalin duniyar ƙwallon ƙafa ya koma kan makomar La liga bayan rabuwa da Messi ɗaya daga cikin shahararrun ƴan ƙwallon da suka ƙayatar da duniya da ƙara wa gasar martaba.

A ranar Lahadi Messi cikin kuka ya yi bankwana da Barcelona da abokan wasansa da kuma magoya bayansa a Spain bayan Barca ta yanke shawarar rabuwa da shi saboda ba ta iya biyansa kuɗin albashi.

La Liga da ake kira gidan Galacticos ta yi shura wajen tara zaratan ƴan ƙwallon duniya musamman saboda ƙarfin Barcelona da Real Madrid manyan ƙungiyoyin Spain da ke hamayya da juna.

Ko da yake rabuwa da shahararren ɗan ƙwallo ba sabon abu ba ne domin zaratan ƴan ƙwallon da Messi ya yi zamani da su sun riga shi sauya sheƙa daga La Liga.

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi sun yi zamanin da tarihin La Liga da hamayyar Barcelona da Real Madrid ba zai taɓa mantawa da su ba.

A 2018, Ronaldo wanda ya fi yawan cin ƙwallaye a tarihin Real Madrid tare da lashe kofin zakarun Turai sau huɗu, ya koma Juventus, matakin da ya ja hankalin duniya. Kuma kamar Messi batun kuɗi na daga cikin dalilin da ya sa Ronaldo ya bar La Liga zuwa Seria A.

Hamayyar a La Liga ta yi zafi zamanin BBC (Benzema da Bale da Cristiano) a Madrid da kuma MSN (Messi da Suarez da Neymar) a Barcelona.

Yanzu Benzema da Suarez kawai suka rage a La liga - Benzema a Real Madrid, Luis Suarez a Atletico Madrid.

Sai dai duk da rabuwa da Ronaldo da sauran zaratan ƴan ƙwallo zamanin BBC da MSN, gasar La liga ta ci gaba da armashi saboda Messi.

Hamayya ta koma tsakanin Messi da Sergio Ramos tsohon kaftin ɗin Real Madrid, bayan tafiyar Ronaldo.

Sai dai Ramos ya koma PSG a watan Yunin 2021 bayan shekaru 16 a Real Madrid.

Yanzu an wayi gari a La liga babu Messi ba Ronaldo da Sergio Ramos kuma babu tabbas kan wasu ƴan ƙwallon da za su gaje su domin armashin gasar.

Ko rashin Messi illa ce?

Messi mai shekara 34, ya shafe shekara 21 a Barcelona tare da lashe kyautar gwarzon ɗan wasan duniya sau shida.

Messi ya ci wa Barcelona ƙwallo 672 a wasa 778, tare da lashe wa ƙungiyar kofuna 35.

Masu sharhi na ganin rashin Messi zai rage wa La Liga daraja da armashi. Amma shugaban La liga Javier Tebas ya ce tafiyar kaftin din na Barcelona da Argentina ba zai sauya komi ba.

Tebas ya ce gasa ba za ta dogara ba a kan wani ɗan wasa ko wata ƙungiya yana mai cewa fitattun ƴan wasa da dama sun tafi kuma ba abin da ya canza.

Ya ba da misali da Ronaldo da Neymar yana mai cewa sun tafi amma gasar Seria A da League 1 da suka koma ba za ta iya gogayya da La Liga ba.

A cewarsa gasar Premier ta Ingila ita ce mafi shahara a duniya kuma ta samu wannan girman ne ba tare samar da gwarzon ɗan wasan duniya ba.

Ya kuma ce duk da abokan hamayyar La Liga za su yi murnar tafiyar Messi amma yana da tabbacin hakan ba zai sauya komi ba.

Sai dai kuma yawancin masu sharhi da masu bibiyar ƙwallon ƙafa na ganin rabuwa da Messi babbar hasara ce ga martabar La Liga.

Wasunsu na ganin La Liga za ta samu nakasu a kuɗaɗen shigarta. Kuma La Liga za ta rage ƙarfi idan aka kwatanta da Seria A mai Ronaldo da kuma gasar da za ta yi babban kamun Messi

Barca - ba Messi

Dubban magoya bayan Barcelona ne suka mamaye harabar gidan Messi domin fatan yin tozali da gwaninsu domin su yi masa bankwana.

An nuna hotunansu sanye da riga mai lamba 10 ta Barcelona.

Ana ganin dimbin magoya bayan Barcelona za su ci gaba da goyon bayan Messi wanda ya lashe masu duk wani kofi da suke buƙata a ƙwallon ƙafa.

A ranar Juma'a za a soma La liga, kuma masu sharhi na ganin rashin Messi wani wagegen giɓi ne a Barcelona.

Barcelona ta fara rayuwa babu Messi a ranar Lahadi kuma ta fara da ƙafar dama.

Barcelona ta doke Juventus ci 3-0 a gasar lashe kofin Gamper, wasan share fagen kaka da suka fafata. Kuma Sabon ɗan wasa Memphis Depay ne ke ci gaba haskakawa a wasannin share fagen kaka inda ya zura ƙwallo a ragar Juventus ana minti uku da soma wasa.

Wannan kan iya zama wata babbar dama ga ƴan wasa masu tasowa, waɗanda sakamakon Messi ba a basu dama domin bajntarsu.