Ronaldo ya kalubalanci Messi ya same shi a Seria A

Dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya kalubalanci Lionel Messi ya bar Barcelona ya dawo wani kulub na Italiya.

Dan wasan na Portugal ya koma taka leda a Seria A a kungiyar Juventus daga Real Madrid kan fam miliyan 99.2.

An dade ana kallon Ronaldo da Messi a matsayin gwarzayen 'yan wasan duniya, inda dukkaninsu suka lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar, kafin Modric ya lashe kyautar a bana.

"Zan so ya zo Italiya wata rana," in ji Ronaldo mai shekara 33.

"Ina fatan zai amince da wannan kalubalen, amma idan yana jin dadi a inda yake, ina girmama hakan."

Ronaldo ya shafe kaka tara a Real Madrid bayan ya baro Manchester United a 2009, yayin da kuma abokin hamayyarsa Messi ya shafe rayuwarsa a Barcelona.

"Da aka tambayi Ronaldo ko yana kewar Messi, sai ya ce: "aa, ai shi ne yake kewa ta."

"Na buga wasa a Ingila da Spain da Italiya da Portugal da kuma tawagar kasa ta, amma Messi har yanzu yana Spain."

"Kila ya fi bukata ta. Ni a waje na, na dauki rayuwa kalubale, ina son haka kuma ina son na dinga faranta wa mutane rai."

"Dan wasa ne mai kyau, amma ban rasa komi ba a nan. Wannan ce sabuwar rayuwa ta."

Na karbi wannan kalubalen a Italiya kuma komi na tafiya daidai, na nuna har yanzu ni dan kwallo ne."