Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Messi ya ci kwallayen da bai taba ci ba
Lionel Messi ya kafa wani tarihin da bai taba kafawa ba a rayuwarsa a wasan da Barcelona ta lallasa Espanyol 4-0.
Messi ya ci kwallaye biyu a raga daga bugun tazara, wanda ya taimakawa Barcelona ci gaba da darewa tebur da tazarar maki uku.
Wannan ne karon farko da kaftin din na Barcelona ya ci kwallaye biyu daga bugun tazara a jere a tarihin rayuwarsa a gasar La Liga.
Kuma Messi ya ci kwallayen ne daga gefe daban-daban, inda ya ci kwallo ta farko a gefen dama, ta biyu kuma daga gefen hagu ana minti 65 da wasa.
Kuma Messi ya kafa wani tarihin inda yake da yawan kwallaye 11 a La Liga, dan wasa na farko da ya ci kwallaye fiye da 10 a kaka 13 a jere.
Messi ya ce zai yi kokarin ci gaba da cin kwallaye daga bugun tazara.
Yanzu dan wasan na Argentina yana da yawan kwallaye 17 a dukkanin wasannin da ya buga wa Barcelona tare da taimakawa a ci sau 10.
Ousmane Dembele ne da Suarez suka zira wa Barcelona sauran kwallayen da ta ci Espanyol.
Nasarar da Barcelona ta samu ya nuna ta shirya wa haduwarta da Tottenham a gasar zakarun turai a ranar talata.