Ben White: Arsenal ta dauki Ben White daga Brighton

ben white

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar Arsenal ta amince ta dauki mai tsaron bayan Brighton & Hove Albion, Ben White kan fam miliyan 50.

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta gayyaci White gasar Euro 2020 daf da za a fara wasannin,

Mai shekara 23 ya koma Brighton daga Southampton, wanda ya buga wasannin aro a Leeds United.

Mai tsaron bayan yana cikin 'yan wasan da suka sa Leeds ta lashe kofin Championship a 2019-20, hakan ne ya sa Brighton ta bashi kwantiragin kaka hudu. .

Kawo yanzu White na hutu, bayan kamala gasar nahiyar Turai da Italiya ta lashe, saboda haka sai ya gama hutun sannan za a kammala yarjejeniyar har da auna koshin lafiyarsa.

An cimma wannan matsaya, bayan da Arsenal ta rabu da dan kwallon tawagar Brazil, David Luiz, wanda kwantiraginsa ya kare a Gunners,

Haka kuma Arsenal ta dauki matashin dan wasa mai shekara 21, Nuno Tavares daga Benfica kan fam miliyan 8.