Abin da kuke son sani kan wasannin karshe a Premier

Ranar Lahadi za a karkare Premier League da za a yi wasa 10, inda za a fayyace wadan da za su wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai a badi.

Tuni dai Manchester City ta lashe kofin bana, yayin da Fulham da West Brom da Sheffield United suka fadi daga gasar bana.

Ranar Lahadi ake sa ran fayyace wadan da za su wakilci Ingila a Champions League da Europa League a badi.

Tuni Manchester City da Manchester United za su buga Champions League a badi, yayin da Leicester City wadda ta lashe FA Cup ta samu gurbin Europa League na badi kai tsaye.

Arsenal da Brighton & Hove Albion

  • Brighton ta doke Arsenal karo uku a wasa bakwai da suka yi a Premier League, har da 2-1 da ta yi nasara a Emirates a bara.
  • Wasa bakwai Arsenal ta ci a karawa 18 da ta yi a gida a bana da canjaras hudu aka doke ta bakwai.
  • Brighton za ta ci gaba da buga Premier a badi, ita kuwa Arsenal wadda ta yi shekara 20 tana buga Champions League a jere a Europa League biyar na son karkare kakar nana cikin masu wakiltar Ingila a gasar Zakarun Turai.

Fulham da Newcastle United

  • Fulham wadda za ta koma buga Championship a badi ta buga wasa tara ba tare da yin nasara ba, inda aka doke ta bakwai da canjaras biyu.
  • Newcastle United ta doke Fulham 4-0 a 2018/19 a wasan karshe, inda Fulham ta fadi daga gasar Premier League a Shekarar nan.
  • Wasa biyar kadai Newcastle ta ci a waje a kakar bana.

Leicester City da Tottenham

  • Leicester City na neman karkarewa a mataki na hudu a bana ta kuma ci wasa 12 iri daya da bajintar da Tottenham ta yi a wasa 29 a haduwar Premier League da suka yi.
  • Watakila Leicester ta yi wa Tottenham gida da waje a bana, bayan da ta doke ta 2-0 a wasan farko a Premier League cikin Disamba.
  • Tottenham na neman gurbin Europa League na badi, kuma ta yi rashin nasara a wasa biyu daga shida da ta buga a Premier League.

Leeds United da West Bromwich Albion

  • West Brom wadda ta fadi daga gasar Premier League ta bana na fatan dfoke Leeds United a karon farko.
  • Wasa na karshe da suka hadu a Elland Road a 2003, West Brom ta tashi 0-0 a karawar, yayin da Leeds ta ci 5-0 a The Hawthorn a farkon kakar bana.
  • Leeds na fatan cin wasa hudu a jere.

Liverpool da Crystal Palace

  • Liverpool wadda ta koma cikin hudun farko a Premier League ta yi nasara a kan Palace a wasa 15 daga 23 da suka fafata a gasar.
  • Liverpool ta caskara Palace 7-0 a Selhurst Park a cikin watan Disamba, bayan da ta yi mata 4-0 a bara cikin watan Yuni.
  • Karawar ita ce ta karshe da kocin Palace, Roy Hodgson zai ja ragamar kungiyar.

West Ham United da Southampton

  • West Ham United ta ci Southampton kwallo uku a wasa uku da suka hadu a tsakaninsu.
  • West Ham ta yi nasara a wasa 18 daga 37 a Premier League da suka fafata a tsakaninsu da canjaras takwas.
  • West Ham ta yi rashin nasara a karawa biyar a gida a kakar bana, inda ta ci wasa tara da canjaras hudu.

Manchester City da Everton

  • Manchester City wadda ta lashe Premier League a bana ta sha kashi da ci 3-2 a gidan Brighton.
  • City za ta buga wasan karshe a Champions League da Chelsea ranar 29 ga watan Mayu.
  • A wasa takwas da City ta yi da Everton ta yi da Everton ta yi nasara a karawa bakwai da canjaras daya.
  • Everton ta ci wasa 11 a waje a kakar bana kamar yadda Leicester City da Manchester United, bayan da City ta ci 14 a fafatawar waje.

Sheffield United da Burnley

  • Burnley ta ci Sheffield United 1-0 a farkon kakar bana, bayan da ta doke ta 3-0 a Premier League a 2019.
  • Daya karawar da suka yi a Premier League tsakanin kungiyoyin sun tashi 1-1 a Turf Moor a 2020.
  • Sheffield United wadda za ta koma buga gasar Championship a badi ta yi nasara a wasa hudu a gida a kakar nan da canjaras daya aka ci ta wasa 13, ita kuwa Burnley wasa shida ta yi nasara a waje.

Aston Villa da Chelsea

  • Wasa biyu kacal Chelsea ta yi rashin nasara daga 10 da ta buga a kwanan nan.
  • Chelsea ta doke Villa sau 26 a wasa 51 a Premier League, inda suka yi 1-1 a bara.
  • Villa ta yi nasara da yawa a wasannin waje fiye da wanda ta buga a bana.
  • Chelsea wadda za ta buga wasan karshe a Champions League da Manchester City na fatan karkare kakar bana cikin 'yan hudun farko.

Wolverhampton Wanderers da Manchester United

  • Kwallo takwas ce ta shiga raga a wasa biyar da suka kara a tsakaninsu.
  • Wasa uku da Wolves ta ci Manchester United a Premier dukka a gida ta yi nasara.
  • Manchester United ta kare a mataki na biyu a Premier bana, duk da 1-1 da ta tashi da Fulham, kuma karo na biyu da ta yi wannan bajintar tun bayan da Sie Alex Ferguson ya yi ritaya a 2013.