Neymar ya tsawaita kwantarinsa da PSG

Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan Brazil da ke taka leda a PSG ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da kungiyar inda ya amince ya ci gaba da taka leda har zuwa 2025, kamar yadda PSG ta sanar.

A 2017 PSG ta ɗauko Neymar daga Barcelona kan makudan kudi yuro miliyan 222.

Neymar kuma ya lashe kofuna 9 a kungiyar tare da taimakawa kulub din zuwa wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a karon farko.

"Na girma na zama mutum anan, na zama cikakken dan kwallo kuma," ya fada a shafin kungiyar ta PSG.

Neymar yana cikin shekarar karshe a kwataraginsa, bayan sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar tun farkon zuwansa.

Tun zuwansa PSG, dan wasan mai shekara 29 ya ci kwallo 85 a wasa 112, kuma ya bayar an ci kwallo 51.

Dan wasan ya fuskanci koma baya a 2019 daga magoya bayan kungiyar wadanda suka rika yi masa ihu, lokacin da ya nuna zai koma Barcelona.

Neymar 'ya fi farin ciki' a rayuwarsa ta PSG.

Neymar ya ce ya samu wani 'gagarumin ci gaba' a zamansa a PSG.

"Na ko yi abubuwa da dama, abubuwa da yawa sun faru da bai kamata su faru ba," in ji shi.

"Mun samu sabani a wasu lokuta, mun fuskanci wasu lokaci marasa dadi, ina farinciki kasacewa cikin tarihin Paris St-Germain.

"Ina fatan kara lashe wasu kofinan da PSG."

PSG, wadda ke kokarin daukar kofinta na hudu a jere, na fukantar tazarar maki hudu tsakaninta da lille da ke matsayi na daya.