Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Mata, Haaland, Odegaard, Icardi, Winks, De Gea, Lingard da Fekir

Juan Mata

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United na shirin bai wa dan wasan tsakiya na Sifaniya Juan Mata, mai shekara 32, karin kwangilar shekara daya. (Star)

Shugaban da ke kula da kwallon kafa Sebastian Kehl ya amince cewa watakila Borussia Dortmund za ta kai wani mataki wanda ba za ta iya ci gaba da rike dan kasar Norway mai shekara 20 Erling Haaland ba. (Goal)

Haaland ya sha gaban dan wasan Barcelona dan kasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, a cikin jerin 'yan kwallon da Manchester City take son dauka duk da yake kocinta Pep Guardiola ya ce kungiyar ba za ta maye gurbin Sergio Aguero, mai shekara 32 ba. (Mirror)

An yi amannar cewa Haaland yana son tafiya Real Madrid amma kungiyar ta Sifaniya ba za ta yi yunkurin daukarsa ba har sai shi da kansa ya nuna sha'awar hakan kana ya nuna cewa zai bar Dortmund. (AS)

WatakilaArsenal ta sayar da matashin dan wasan Ingila Bukayo Saka, mai shekara 19, domin ta samu kudin sayen dan wasan Real Madrid dan kasar Norway Martin Odegaard, mai shekara 22, a mataki na dindindin, sannan ta sayi karin 'yan wasa domin yin garambawul a kungiyar. (Times - subscription required)

Manchester United za ta biya golan Sifaniya David de Gea makudan kudade a matsayin kudin sallama a yayin da dan wasan mai shekara 30 yake shirin barin Old Trafford ia bazarar nan. (Mirror)

Kazalika Manchester United tana sondan wasan Paris St-Germain da Argentina Mauro Icardi, mai shekara 28 domin maye gurbin Edinson Cavani, mai shekara 34. (Teamtalk)

Atletico Madrid na sha'awar daukar dan wasan Tottenham da Ingila Harry Winks, mai shekara 25, wanda ya yi ta fafutukar ganin ya rika mruza leda a kai-a kai a lokacin jagorancin Jose Mourinho. (Sky Sports)

KocinWest Ham David Moyes bai damu ba game da yarjejeniyar aron dan wasan Manchester United da Ingila Jesse Lingard, mai shekara 28, wacce ba ta ba su damar sayensa ba. (Mail)

Manchester United na duba yiwuwar daukar dan wasan Portugal mai shekara 18 Nuno Mendes daga Sporting Lisbon kuma za ta iya mika dan wasan Brazil mai shekara 28 Alex Telles a matsayin musaya (Record - in Portuguese)

Barcelona na tunanin daukar dan wasan Real Betis dan kasar Faransa Nabil Fekir amma ana alakanta dan wasan mai shekara 27 da son tafiya Arsenal. (Estadio Deportivo)