Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Sancho, Wijnaldum, Neuhaus, Balogun, Vieira, Costa, Gibbs
Liverpool na shirin rabuwa da Georginio Wijnaldum, dan wasan tsakiya da kasar Netherlands mai shekara 30, kuma suna son dauko Florian Neuhaus, ya maye gurbinsa daga Borussia Monchengladbach wanda dan shekara 29 ne. (Kicker)
Kocin Liverpool Jurgen Klopp kuma na iya dauko Rodrigo de Paul, dan wasan Udinese mai shekara 26, kuma dan kasar Argentina kan fam miliyan 30. (Sun)
Arsenal na ganin za su iya rarrashin Folarin Balogun, dan wasan gabansu mai shekara 19 ya yi zamansa a kungiyar. Kwantiraginsa ta kusa karewa kuma akwai kungiyoyin da ke zawarcinsa daga sassan Turai. (London Evening Standard)
Bayer Leverkusen ma na cikin masu bukatar daukar Balogun inda Stuttgart and Rennes ma sun bayyana sha'awarsu ta dauke shi daga Emirates . (Mirror)
Akwai tabbaci ɗan wasan gefe na Borussia Dortmund Jadon Sancho zai koma wata kungiya a kakar wasan baɗi, amma da wuya a smi wanda zai biya kungiyar ta kasar Jamus £100 kan dan wasan mai shekara 20, kuɗin da su ka bukaci Manchester Unitedta biya wata shida da ya gabata. (Eurosport)
Lucas Digne, dan wasan baya na Everton mai shekara 27 ya amince ya tsawaita kwantiraginsa tare da Toffees. (Sky Sports)
Martin Keown ya ba Bournemouth shawara cewa su dauki Patrick Vieira, tsohon dan wasan Arsenal mai shekara 44 ya horar da 'yan kwallon ƙungiyar tun da ba su da mai horarrwa a yanzu. (Talksport)
Diego Costa, wanda ya bar Atletico Madrida Disambar bara na tattaunawa da Palmeiras ta Brazil domin ya koma can - Palmeiras ce kungiyar da ya goya wa baya a lokacin yana karamin yaro. (Sky Sports)
Mai tsaron gidan Aston Villa Emiliano Martinez, ya kamanta Jack Grealish dan wasan Ingila mai shekara 25 da tauraron Barcelona Lionel Messi. (Talksport)