Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Eriksen, Upamecano, Alli, Odegaard, Jose, Sane, Caicedo

Asalin hoton, Getty Images
Leicester City ta sauya ra'ayinta kan dauko Christian Eriksen, dan wasan tsakiya na Inter Milan mai shekara 28 saboda yawan albashin dan kasar Denmark din da ya kai fam 300,000 a mako. (Telegraph)
Bayern Munich ta bayyana aniyarta ta daukan Dayot Upamecano, dan wasan RB Leipzig mai shekara 22 kuma dan kasar Faransa, amma akwai fam miliyan 40 da duk mai son sayensa zai biya. (Mirror)
Manchester United, Manchester City da Chelsea duka sun nuna sha'awarsu kan Upamecano, amma ba za a sayar da shi ba sai karshen wannnan kakar wasan. (Goal)
Dan wasan Tottenham da Ingila, Dele Alli mai shekara 24 ya roki mai kungiyar Daniel Levy da ya kyale shi ya koma Paris St-Germain. (90min)
Arsenal na son dauko wanda zai gaji Kieran Tierney, dan wasan baya mai shekara 23 kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa ami ci a yanzu. (Express)
Dan wasan Real Madrid mai shekara 22 Martin Odegaard ya kusa komawa Arsenal duk da cewa wasu na zawarcin dan kasar Norway din. (Sport - in Spanish)
Dan wasan tsakiya na Ecuador Moises Caicedo mai shekara 19 na kan hanyar zuwa Ingila domin kammala shirin komawarsa Brighton daga Independiente del Vallekan fam miliyan 4.5. (Sky Sports)
Kocin Real Sociedad Imanol Alguacil na fatan Willian Jose, dan wasan gaba na kungiyar zai buga wasa duk da cewa Wolves na son saye shi. (Marca, via Birmingham Mail)
Tilas Wolves su biya kimanin fam miliyan 17 kafin su iya sayen Jose ya kuma zama dan wasansu na din-din-din. (Express & Star)
Everton na son a biya su fam miliyan 9 kafin su sayar da Bernard, dan wasan tsakiya da kasar Brazil mai shekara 29. (Telegraph)











