Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Odegaard, Smith Rowe, Lingard, Garcia, Lampard, Rose

Arsenal sun fara tuntuba an Martin Odegaard dan wasan Real Madrid da Norway mai shekara 22. (Sky Sports)

Sai dai ana cewa Odegaard ya kusa komawa Sevilla a matsayin dan wasa na aro. (Cuatro - in Spanish)

Arsenal ta shirya yi wa dan wasanta na tsakiya Emile Smith Rowe mai shekara 20 sabuwar kwantiragi na fam 40,000 a kowane mako. (Mail)

Tottenham, West Ham da Sheffield United na cikin kungiyoyi da ke rige-rigen dsaukar Jesse Lingard, dan wasan tsakiya mai shekara 28 daga Manchester United a matsayin dan aro. (Talksport)

Paris St-Germain kuwa sun shirya tsaf domin ba da mamaki wajen dauke Eric Garcia, dan wasan Manchester City da Spaniya mai shekara 20. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Chelsea ba ta son sauya kocinta Frank Lampard da wani sabo ana tsakiyar kakar wasa, duk da cewa ya gaza ba su abin da su ke bukata. (Independent)

Amma za a kori Lampard idan sakamakon da kungiyar ke samu ba su inganta ba nan da wani lokaci. (Sky Sports)

Kelechi Iheanacho, dan wasan Leicester mai shekara 24 da Divock Origi na Liverpool mai shekara 25 da kuma Kasper Dolberg, dan wasan gaba na Nice na cikin 'yan wasan da RB Leipzig ke bukata. (Bild - via Leicester Mercury)

Danny Rose, dan wasan baya na Ingila da Tottenham kuwa na ciin 'yan wasan da Trabzonsporta Turkiyya ke sha'awar dauka. (Mail)

AC Milan ta kusa cimma yarjejeniya kan daukan Fikayo Tomori, dan wasan baya na Chelsea mai shekara 23 amma a matsayin dan aro. (Gazzetta dello Sport)