Messi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar La Liga

Kyaftin din Barcelona, Lionel Messi, ya dare mataki na daya a cin kwallaye a gasar La Liga, wadda ake buga karawar mako na 18.

Ranar Asabar Barcelona ta je ta yi nasara a kan Granada da ci 4-0, kuma Messi ne ya ci kwallo biyu a wasan na La Liga.

Dan kwallon Argentina mai shekara 33 ya ci kwallo 11 a La Liga ta bana sannan ya bayar an ci biyu.

Gerard Mreno na Villareal ne ke biye masa da ƙwallo 10, sai Lago Alpas da Luis Suarez masu tara-tara, da kuma Karim Banzema mai takwas.

Messi ya lashe kyautar Pichichi wato ta dan wasan da ya fi cin kwallo a gasar La Liga karo bakwai.

Dan kwallon Barcelona ya yi shekara 15 yana cin kwallaye fiye da 10 a kowacce kakar tamaula da babu wanda ya yi wannan wajintar.

Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 34, Real ce ta biyu mai maki 37, yayin da Atletico ke jan ragama maki 38 tare da kwantan wasa uku.