Ko Real Madrid za ta karkare 2020 da cin wasa bakwai a jere?

Real Madrid za ta ziyarci Elche domin buga wasa na 16 a gasar cin kofin La Liga ranar Laraba kuma na karshe a shekarar 2020.
Real wadda ta yi wasa 15 tana mataki na biyu a teburi da maki 32 iri daya da na Atletico Madrid wadda take ta daya mai wasa 13.
Wannan shi ne wasa na takwas da Real Madrid za ta buga a cikin watan Disamba kuma na karshe a 2020 har da rashin nasara da ta yi a hannun Shakhtar a Champions League.
Ranar 1 ga watan Disamba Real ta yi rashin nasara a gidan Shaktar da ci 2-0, tun daga nan ta yi fafatawa biyar a La Liga da Champions League a jere ta kuma yi nasara a dukkan karawar.
Ta fara da doke Sevilla da ci 1-0 ranar 5 ga watan Disamba, sai kuma ta yi nasara a kan Borussia Munchengladbach 2-0 ranar 9 ga watan Disamba.
Daga nan ne Real ta doke Abokiyar hamayya Atletico Madrid da kuma Athletic Bilbao da Eibar da kuma Granada duk a gasar La Liga a cikin watan Disambar.
Wasan da Real za ta ziyarci Elche shi ne na karshe a 2020, tuni kuma Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 24 da za su buga masa fafatawar.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da E. Militao da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Odegaard.
Masu cin kwallaye: Hazard da Benzema da Asensio da Lucas V. da Jovic da Vini Jr. da kuma Mariano.











