La Liga: Barcelona ta koma ta 10 a teburin bayan Atletico ta doke ta

Atletico v Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yannick Carrasco ne ya ci wa Atletico ƙwallon ɗaya tilo

Atletico Madrid ta kamo Real Sociedad a saman teburin La Liga bayan ta doke Barcelona, wadda yanzu aka ba ta tazarar maki tara daga saman teburin.

Yannick Carrasco ne ya ci ƙwallo ɗaya tilo ana ƙoƙarin tafiya hutun rabin lokaci lokacin da ya jawo ƙwallo tun daga kusan tsakiya zuwa ragar mai tsaron raga Marc-Andre ter Stegen.

Haka nan ɗan wasan bayan Barca Gerard Pique ya ji rauni, abin da ya ƙara wa ƙungiyar gishiri a nata raunin na daren Asabar.

Barca ta tabbatar bayan wasan cewa Pique ya turguɗe gwiwarsa ta dama "sannan yana buƙatar ƙarin gwaje-gwaje domin tantance raunin".

Babu tabbacin lokacin da Pique zai ɗauka na jinya amma rahotanni daga Spain na cewa zai iya kaiwa wata shida.

Da wannan nasara, Atletico ta ci gaba da jan ragamar wasanni ba tare da an doke ta ba a kakar wasa ta bana, inda ta buga jumillar wasa 24 a kowace gasa ba tare da rashin nasara ba.

Lionel Messi bai taɓuka komai ba a wasan duk da cewa ya dawo ne daga tafiya mai nisa bayan ya buga wa ƙasarsa wasa.

Teburin la Liga

Yanzu haka Atletico Madrid da Real Socieded ne ke jan ragamar teburin da maki 20 kowaccensu.

Barcelona na mataki na 10 da maki 11, yayin da Real Madrid wadda ta buga 1-1 da Villareal ke mataki na 4 da maki 17.