Jordi Alba ya bayar da kwallo 63 aka zura a raga a kaka takwas a Camp Nou

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Barcelona, Jordi Alba ya zama na biyu wajen bayar da kwallo a zura a raga a kungiyar.
Dan wasan mai tsaron baya ya bayar da kwallo 63 aka zura a raga har da hudu a wasa shida da ya buga a bana.
Jordi Alba, mai shekara 31, mai tsaron baya ya koma Camp Nou daga Valencia ranar 28 ga watan Yunin 2012.
Dan wasan ya buga wa Barcelona wasa 211 a La Liga, inda ya yi sauyi sau 19 ya kuma ci kwallo 10 kawo yanzu.
Dan wasa ne mai tsaron baya daga gefe, amma yana da kokarin jan kwallo zuwa gaba ya kuma kware wajen bai wa abokin wasa kwallon da zai zura a raga daga buhu sai tukunya.
Ranar 26 ga watan Agustan 2012 Alba ya bai wa Messi kwallon da ya ci Osasuna saura minti takwas a tashi wasa, tun daga nan ya ci gaba da sa kwazo a kungiyar.
Ko a lokacin da Luis Suarez ke buga wa Barcelona tamaula, sai da Alba ya ba shi kwallo sau 20 yana zura wa a raga.
Kawo yanzu Alba ya bayar da kwallo 63 da aka ci a Barcelona da suka hada da 46 a La Liga da tara a Champions League da guda takwas a Copa del Rey.
Kyaftin din Argentina, Lionel Messi shi ne kan gaba a bayar da kwallo a zura a raga, sai Jordi Alba na biyu a Barcelona.
Kakar da Alba ya fi yin bajinta ita ce ta 2018/19 da ya bayar da kwallo hudu aka zura a raga a farkon wasa takwas da ya fafata.











