Sergio Ramos ya yi wa tawagar kwallon kafa ta Spaniya wasa 177

Sergio Ramos

Asalin hoton, Getty Images

Serio Ramos ya zama kan gaba a nahiyar Turai wajen buga wa tawagar kwallon kafa wasanni, bayan da ya yi wa Spaniya wasa 177.

Ranar Asabar Switzerland ta karbi bakuncn Spaniya a wasan Uefa Nattions League, inda suka tashi karawar 1-1.

Kawo yanzu Ramos wanda ya barar da fenariti biyu a wasa da Switzerland ya haura Gianluigi Buffon na Italiya wajen yawan buga wasanni.

A baya dai kyaftin din na Real ya ci kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga sau 25 da ya yi a tawagar Spaniya da kungiyar Madrid.

Mai masukin baki, Switzerland ce ta fara cin kwallo ta hannun Remo Freuler a minti na 26 da fara tamaula.

Switzerland ta karasa fafatawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Nico Elvedi katin gargadi na biyu da bugun fenariti na biyu, bayan da ya yi wa Morata keta.

Spaniya ta farke kwallo daf da za a tashi ta hannun Gerard Moreno, bayan da Sergio Reguilon ya buga masa kwallon.

Kawo yanzu Spaniya na bukatar doke Jamus ranar Talata a Sevilla idan har tana son kai wa karawar Nations League ta badi..