Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Semedo, Ramos, Boateng, Arteta, Garcia, Isco, Jimenez
Liverpool ta shirya tuntubar Olympiakos da zummar daukar dan kasar Portugal Ruben Semedo, mai shekara 26, domin cike giɓin da ta samu sakamakon jinyar da Virgil van Dijk da Joe Gomez suke yi. (Sic Noticias, via Express)
ShugabanReal Madrid Florentino Perez da kyaftin na kungiyar Sergio Ramos za su yi jawabi ranar Litinin kan makomar dan wasan na Sifaniya mai shekara 34. (AS)
Dan wasanBayern Munich Jerome Boateng, mai shekara 32, ya bayyana mamakinsa game da jita-jitar da ke cewa zai bar kungiyar a karshen kakar wasan bana domin tafiya Tottenham. (Suddeutsche Zeitung, via Teamtalk)
Manchester United na son daukar dan wasan Braga mai shekara 21 dan kasar Portugal David Carmo a yayin da suke neman dan wasan baya na gefe. (ESPN, via Mail)
Kocin Everton Carlo Ancelotti zai kara kaimi wurin ganin ya dauko dan wasan Real Madrid dan shekara 28 dan kasar Sifaniya Isco domin kawo shi Goodison Park. (Le10 Sport - in French)
Dan wasan Sifaniya Eric Garcia ya yi gum da bakinsa kan makomarsa a Manchester City a yayin da ake ci gaba da rade-radin cewa dan kwallon mai shekara 19 zai koma Barcelona. (El Mundo, via Manchester Evening News)
Dan wasan Wolves da Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29, ya bayyana cewa Manchester United na cikin kungiyoyin da suka yi yunkurin daukarsa a bazara. (TUDN, via Metro)
Rahotanni na cewa Manchester United na shirin dauko dan wasan Borussia Dortmund Dan-Axel Zagadou a bazara da ke tafe. (Calciomercato, via Manchester Evening News)
Dan wasan Everton dan kasar Turkiyya Cenk Tosun, mai shekara 29, ba ya tunanin komawa Besiktas, ko da yake zai iya sauya matsayinsa idan Eveton ta dauki wani dan wasan gaba. (asistanaliz.com, via Sport Witness)
Dan wasan Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, ya ce bai yi wani kokwanto ba a kan tafiya Arsenal daga Lille a watan Satumba lokacin da aka nemi ya tafi kungiyar. (Arsenal Player, via Standard)
Tsohon dan wasan Newcastle United da Ingila John Barnes ya yi amannar cewa idan kungiyar ta gama kakar wasan bana a tsakiyar tebirin Firimiya za ta yi san-barka. (PlayOjo, via Newcastle Chronicle)
Daraktan wasanni naBorussia Monchengladbach Max Eberl ya yi watsi da rahotannin da ke cewa dan kasar Jamus mai shekara 23 Florian Neuhaus zai bar kungiyar zuwa Bayern Munich. (Sport1, via Goal)
Tsohon dan wasan Arsenal Cesc Fabregas ya yi amannar cewa kocin kungiyar Mikel Arteta yana fuskantar matsin lamba yana mai cewa akwai bukatar ya zage dantse domin ganin sun taka rawar gani sosai. (90min)