Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohamed Salah: Ɗan wasan Liverpool gwaji ya tabbatar ya kamu da korona
Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah gwaji ya tabbatar da yana ɗauke da cutar korona yayin da ya tafi bugawa ƙasarsa wasa
Hukumar ƙwallon Masar ce ta tabbatar a ranar Juma'a cewa Salah mai shekara 28, sakamakon gwajin korona da aka yi masa ya nuna yana ɗauke da cutar.
Hukumar ta ce sauran ƴan wasan gwaji ya nuna ba su ɗauke da korona.
Masar za ta karɓi bakuncin Togo a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika a ranar Asabar.
Yanzu Salah zai killace kansa kuma zai ƙauracewa buga wa Liverpool wasanni na tsawon mako biyu
A ranar Asabar Liverpool za ta karɓi baƙuncin Leicester a Premier League kafin ta haɗu da Atalanta a Anfield a gasar zakarun Turai.
Salah a bana ya buga wa Liverpool dukkanin wasanninta a Premier inda ya ci kwallaye takwas