Josep Maria Bartomeu ya ajiye aikin shugabancin Barcelona

Shugaban Barcelona, Josep Maria Bartomeu ya sauka daga mukamin, bayan matsin lamba daga magoya baya kan sabani tsakaninsa da Lionel Messi.

Bartomeu, wanda ya zama shugaban Barcelona a 2014, ya ajiye aikin, bayan da magoya baya ke kokarin hambarar da shi.

Shugaban ya samu sabani tsakaninsa da kyaftin din Argentina, Lionel Messi, wanda ya bukaci barin Barcelona kan fara kakar bana ta tamaula.

Ya ajiye aikin ne kwana uku da Barcelona ta sha kashi a hannun Real Madrid da ci 3-1 a Gasar La Liga karawar hamayya ta El Clasico a Camp Nou.

Cikin watan Maris ya kamata Bartomeu ya sauka daga shugabancin Barcelona, bayan wa'adin zango biyu.

Messi ya ce Bartomeu ya yaudare shi, bayan da batun barin Barcelona ya bi ruwa.

A karkashin shugabancinsa, Barcelona ta lashe kofin La Liga hudu da Champions League a 2015.