El Clasico: Tun bayan da Ronaldo ya bar Spaniya, Messi bai ci Real ba

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Ranar Asabar Real Madrid ta doke Barcelona a Camp Nou da ci 3-1 a gasar La Liga, kuma Messi bai ci kwallo a wasa takwas a El Clasico ba.

Ansu Fati ne ya ci wa Barcelona kwallo a karawar da ta sha kashi a gida a wasan na La Liga na hamayya tsakanin manyan kungiyiyoyin kwallon kafar Spaniya.

Rabon da Messi ya ci Real a karawar ta El Clasico tun 2-2 da suka tashi a Camp Nou, karawar mako na 36 a gasar La Liga kakar 2017-18.

Hakan na nufin Messi bai zura kwallo a ragar Real Madrid ba tun bayan da Cristiano Ronaldo ya koma Juventus.

A karawaer ta El Clasico Messi na kan gaba a cin kwallaye da 26, wanda ya ci 18 a La Liga da shida a Super Cup da kuma biyu a gasar Zakarun Turai.

Kafin Cristiano ya bar Spaniya shi ne ke mataki na uku a cin kwallaye a wasan na hamayya da 18 a raga, mai guda tara a La Liga da biyar a Copa del Rey da kuma hudu da ya ci a Super Cup.

A kakar bana, kwallo daya kacal Messi ya ci wa Barcelona a gasar La Liga, shi ne wasan farko da ta fara kakar bana da Villareal.

Tun daga nan bai zura kwallo a raga ba ko kuma bayar wa a ci a wasa hudu da ya buga, ya taba yin irin wannan rashin kokarin a kakar 2014.

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Tun kan fara kakar bana, Messi ya bukaci barin Barcelona domin gwada kwazonsa a wata kungiyar, inda wasu rahotanni ke cewar Manchester City ta yi shirin sayen dan kwallon.

Barcelona ta kasa lashe kofi a bara, bayan da take ta daya a kan teburin La Liga, Real Madrid ta karbe gurbin, bayan jinyar cutar korona ta lashe kofin gasar ta Spaniya ta bara.

An sa rana Barcelona za ta sa karfi a Gasar Zakarun Turai ta Champions League, sai Bayern Munich ta dura marta 8-2 a Agustan bara, daga nan abubuwa suka kara balbalcewa kungiyar ta Camp Nou.

Haka kuma Messi ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Argentina kwallo daya a wasa biyu a bana shi ne da Ecuador cikin watan Oktoba a wasan neman gurbin shiga Gasar cin kofin duniya da za a yi a 2020.

Wasa biyar nan gaba da Barcelona za ta fafata:

Laraba 28 ga Oktoba Champions League

  • Juventus da Barcelona

Asabar 31 ga watan Oktoba La Liga

  • Alaves da Barcelona

Laraba 4 ga watan Oktoba Champions League

  • Barcelona da Dynamo Kiev

Asabar 7 ga watan Nuwamba La Liga

  • Barcelona da Real Betis

Lahadi 22 ga watan Nuwamba La Liga

  • Atl Madrid da Barcelona