Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Son, Ings, Sarri, Jones, Zabaleta, Dybala, Haaland

Son Heung-min

Asalin hoton, Getty Images

Tottenham na shirin kara alawus din mako-mako na Son Heung-min zuwa £150,000 a yunkurin rarrashin dan wasan na Koriya ta Kudu, mai shekara 28, ya tsawaita zamansa a kungiyar. (Mail)

Dan wasanSouthampton da Ingila Danny Ings, mai shekara 28, yana dab da tsawaita zamansa a kungiyar a yayin da Tottenham ke zawarcinsa.(Athletic - subscription required)

Liverpool na son dauko dan wasan Brighton dan kasar Ingila Ben White bayan Leeds United ta gaza daukarsa duk da cewa sau uku tana son dauko dan wasan mai shekara 23 a bazara. (Football Insider)

Arsenal ta nemi dauko dan wasan Sporting Lisbon dan kasar Portugal mai shekara 17 Joelson Fernandes a lokacin musayar 'yan kwallon kafa. (Football London)

Tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri ne a kan gaba a wadanda za a bai wa ragamar jagorancinFiorentina idan suka kori Giuseppe Iachini. (Calcio Mercato - in Italian)

Manchester City za ta amince tsohon dan wasanta Pablo Zabaleta ya koma kungiyar domin aiki da ita amma ban da murza leda bayan dan kasar argentina mai shekara 35 ya yi ritaya a makon jiya. (Mail)

Dan wasan Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, zai gwammace tafiya Real Madrid maimakon Manchester United. (ABC via Manchester Evening News)

Barcelona tana son sayar da dan wasan Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23, da dan wasan Denmark Martin Braithwaite, mai shekara 29, domin dauko 'yan wasa biyu 'yan kasar Netherlands - dan wasan Lyon Memphis Depay, mai shekara 29, da dan wasan AZ AlkmaarMyron, mai shekara 19. (Todofichajes - in Spanish))

Juventus na da kwarin gwiwar dan wasan Argentina Paulo Dybala, mai shekara 26, zai tsawaita zamansa. (Tuttosport - in Italian)

Dan wasanManchester United Phil Jones, mai shekara 28, yana son barin kungiyar a watan Janairu, bayan ya fusata kan cire shi daga cikin tawagar da za ta buga gasar Champions League. (Sun)

Paris St-Germain za ta yi yunkurin sayen dan wasan Inter Milan Christian Eriksen, mai shekara 28, a kan euro 20m (£18.1m), a yayin da dan kasar ta Denmark ke fafutukar ganin an rika sanya shi a wasa a kai- a kai kungiyar da ke buga gasar Serie A. (Todofichajes - in Spanish)