PSG VS Man United: Gasar Champions League karawar rukunin farko

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Manchester United za ta buga gasar Champions League ta bana a karon farko tun bayan wata 18, inda za ta ziyarci Paris St-Germain ranar Talata a Faransa.
Paris St-Germain wacce ta lashe kofi uku a bara a gasar Faransa ta kai karawar karshe a Champions League, sai dai Bayern Munich ce ta doke ta lashe kofin da aka ƙarƙare.
United za ta buga wasan da ƙarfin gwiwa, bayan da ta doke Newcastle United 4-1 ranar Asabar a gasar Premier League, bayan da ta sha kashi a gida da ci 6-1 a hannun Tottenham.
Kungiyoyin biyu suna rukuni na takwas da ya hada da RB Leipzig da kuma Istanbul Basaksehir F.K
Paris St-Germain
Kungiyar ta Faransa ta fara kakar Ligue 1 ta Faransa 'yan ƙwallonta sun gaji saboda buga Champions League da kungiyar ta yi. Saboda haka wasu 'yan wasan sun dan yi hutu wasu kuma sun killace kansu don gudun yada cutar korona kamar yadda doka ta bukata.
Hakan ne ya sa PSG ta yi rashin nasara a wasa biyu da ta fara buga wa a gasar Faransa ta bana, inda ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Lens da kuma wanda Marseille ta doke ta - a karawar ce aka bai wa Neymar jan kati.
Daga nan ne PSG ta koma kan ganiyarta har ma ta doke Metz da Nice da Reims da Angers da kuma Nimes, sannan ta ci kwallo 16 aka zura mata daya a raga ta koma ta biyu a kan teburi biye da Lille ta daya.
Manchester United

Asalin hoton, Getty Images
Ita kuwa Manchester United tana ta 14 a kasan teburin Premier League na shekarar nan da maki shida, bayan cin wasa biyu da rashin nasara biyu.
United ta yi cefane da yawa da ake ganin za ta taka rawar gani a a bana, sai kuwa Crystal Palace ta je ta doke ta 3-1 a Old Trafford, sai kuma ta je ta yi nasara a gidan Brighton da ci 3-2 a gasar Premier League da kuma nasara a kan Newcastle da ci 4-1 ranar Asabar a wasan da suka fafata a St James Park.
Haka kuma United ta sha kashi a gida da ci 6-1 a hannun Tottenham, amma United ta yi nasara a kan luton da Brighton a gasar Caraboa Cup.
Labarai daga PSG
Mauro Icardi ba zai buga karawar ba, yayin da Marquinhos da Thilo Kehrer da Marco Verratti da kuma Julian Draxler ba su yi wa PSG wasan da ta doke Nimes 4-0 ranar Juma'a ba.
Shi kuwa dan kwallon da ta dauka aro daga Porto, Danilo Pereira ya killace kansa, bayan da ya koma Faransa, sakamakon buga wa kasarsa tamaula da ya yi, amma ya yi atisaye ranar Lahadi.
Labarai daga Manchester United
Anthony Martial wanda aka yi wa jan kati a karawa da Tottenham zai buga wasa da PSG ranar Talata, haka kuma sabon dan kwallon da ta dauka Edinson Cavani da Alex Telles da kuma Facundo Pellistri suna cikin 'yan wasan da United ta saka cikin wadanda za su buga mata gasar zakarun Turai ta bana, watakila su fara yi mata wasan farko a ranar Talata.

Asalin hoton, Getty Images
Neymar da kuma Mbappe fitattun 'yan wasa ne a duniya da ke kan ganiya a yanzu haka, kuma su biyu sun ci kwallo 150 a dukkan wasannin da suka yi wa PSG tun lokacin da suka koma kunguiyar a 2017.
Neymar bai buga wasa biyu da aka fafata tsakanin PSG da United ba, sakamkon jinya, shi kuwa Mbappe ya buga dukkan wasan biyu, shi ne ma ya ci wa PSG kwallo na biyu a Old Trafford kuma shi ne dan wasa mai hatsari a fafatawar har sai da ya buga kwallo ta bugi turke a karawar da suka tashi 2-0.
Mbappe dan wasan tawagar Faransa ya yi wasa hudu a bana ya kuma ci ƙwallo hudu, shi kuwa dan wasan tawagar Brazil, Neymar ya ci kwallo biyu a wasa uku a bana.
Haduwa tsakanin kungiyoyin biyu
PSG ta je Old Trafford ta yi nasara da ci 2-0 a wasan farko a gasar Champions League a 2018/19, karawar kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.
A wasa na biyu United ta je Faransa ba tare da fitattun 'yan kwallonta da suka hada da Paul Pogba da aka dakatar da Anthony Martial da ya yi jinya, kuma tana bukatar cin kwallo biyu a kalla.
Daga karshe United ta yi nasara da ci 3-1 a fafatawar da suka yi ranar 6 ga watan Maris, 2019.
Wadanda za su ja ragamar wasan:
Alkalin wasa: Antonio Mateu Lahoz
Mataimakansa: Pau Cebrian Devís da kuma Roberto del Palomar
Mai jiran ko ta kwana: Javier Estrada Fernandez
Mai kula da VAR: Juan Martinez Munuera
Mataimakinsa: Guilllermo Cuadra Fernandez
Gasar Champions League da za a kara ranar Talata 20 ga watan Oktoba
- Chelsea da Sevilla
- Rennes da FK Krasnodar
- Zenit St Petersburg da Club Brugge
- Lazio da Borussia Dortmund
- Dynamo Kiev da Juventus
- Barcelona da Ferencvaros
- Paris Saint Germain da Man United
- RB Leipzig da Istanbul Basaksehir
Ranar Laraba 21 ga watan Oktoba
- RB Salzburg da Lokomotiv Moscow
- Bayern Munich da Atletico Madrid
- Real Madrid da Shakhtar Donetsk
- Inter Milan da Borussia Monchengladbach
- Manchester City da FC Porto
- Olympiacos da Marseille
- Ajax da Liverpool
- FC Midtjylland da Atalanta











