Jerome Prior: An ciji mai tsaron raga a gasar Faransa ta rukuni na biyu

Ousseynou Thioune

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An zargi dan wasan Sochaux, Ousseynou Thioune da gartsa cizo a lokacin wasa

Ana zargin wani dan kwallo da cizon mai tsaron raga a lokacin gasar Faransa ta 'yan rukuni na biyu.

A wasan da suka buga ranar Asabar, an bar mai tsaron ragar Valenciennes, Jerome Prior dauke da jini a kumatunsa, inda kungiyar ta zargi dan wasan Sochaux, Ousseynou Thioune da yin cizon.

"An gartsa wa Jerome cizo a kumatunsa," Kamar yadda shugaban Valenciennes, Eddy Zdziech ya shaida wa kafar yada labarai ta AFP.

"Irin wannan halayyar abu ne da ya kamata a dauki babban mataki.

An yi hayaniya a cikin fili a lokacin da aka tashi daga wasan da suka tashi ba ci, inda kocin Valenciennes, Olivier Guegan ya ce an ciji golan a kumatu ne a lokacin da aka kwaso kwana.

Sai dai kuma kocin Sochaux, Omar Daf ya kare mai tsaron bayansa dan kasar Senegalese, Thioune, da cewar ya dai ji cacar baki.

"Dan wasa ba zai harzuka haka kawai har sai an yi masa wani abu, in ji Daf.

"Na ji kalaman cin zarafi a karshen wasan, amma ya kamata a samu kamun kai."

Goalkeeper Jerome Prior dives for a ball in 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mai tsaron raga Jerome Prior a lokacin atisaye a 2018