Wasan sada zumunta: Karon farko da Najeriya za ta kara da Tunisia tun bayan kofin Afirka

Tawagar kwallon kafa ta Najeria za ta buga wasan sada zumunta da ta Tunisia ranar Talata a Austria.

Wannan ne wasa na biyu da Najeriya za ta buga tun bayan wata 11 da ta je ta doke Lesotho da ci 4-2 a karawar neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

A ranar Juma'a Algeria mai rike da kofin nahiyar Afirka ta doke Super Eagles da ci 1-0 a wasan sada zumunta da suka kara a Austria.

Super Eagles na buga wasannin ne don shirin tunkarar karawa da Saliyo a cikin watan Nuwambar 2020 a fafatawar neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Ramy Bensebaini ne ya ci Algeria kwallon da ya bai wa koci Djamel Belmadi dama ta biyu da ya yi nasara a kan Najeria har da ta gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka kara a Masar.

Nigeria ta yi nasara a kan Tunisia da ci 1-0 a wasan neman mataki na uku da suka fafata a Cairo a 2019, kuma Odion Ighalo ne ya ci wa Super Eagles kwallon.

Wasu wasannin sada zumunta da za a buga ranar Talata:

  • Japan da Ivory Coast
  • Morocco da Jamhuriyar Dumukaradiyyar Congo
  • Mexico da Algeria