Da gaske korona ta kama ƴan wasan Super Eagles?

Lokacin karatu: Minti 1

Hukumar kwallon ƙafar Najeriya ta ƙaryata labarin da wasu jaridun ƙasar suka buga cewa wasu ƴan wasa huɗu daga cikin tawagar Super Eagles sun kamu da korona kafin wasan sada zumunci da za su yi da Algeria ranar Juma'a.

Hukumar ta ce labarin ƙarya ne, kamar yadda ta wallafa a Twitter.

A labarin da Sahara Reporters ta buga a shafinta ta ce kocin Super Eagles yayin ganawa da manema labarai ne ya sanar da cewa ƴan wasa huɗu sun kamu da korona, ba tare da ya bayyana sunayen ƴan wasan ba.

Amma hukumar NFF ta ce ba a fahimci bayanin kocin Super Eagles Gernot Rohr ba, inda hukumar ta ce kocin yana nufin tun ɓarkewar annobar korona ƴan wasa huɗu ne suka kamu da cutar.

"Amma dukkaninsu sun warke," in ji NFF

Hakan dai na nufin ƴan wasan sun warke bayan sun kamu da korona.

Hukumar NFF ta ce tana jiran sakamakon gwajin da aka yi wa ƴan wasan kafin karawar da za su yi da Algeria.