Real Madrid: Wasa 15 a jere ba a doke ta ba a La Liga tun bayan cutar korona

A wannan lokacin gasar kasashen duniya na hutu bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta amince a buga gasa ko wasannin sada zumunta tsakanin tawagogin kwallon kafa a fadin duniya.

Hakan ne ya sa zamu yi duba na tsanaki kan kwazon Real Madrid wacce ba ta sayi dan kwallo ko daya ba a bana duk da cinikayyar da aka gudanar, inda aka rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ranar 5 ga watan Oktoba.

Tuni dai Real Madrid ta yi wasa 15 a jere a gasar La Liga ba a doke ta ba, tun bayan jinyar cutar korona, kuma kawo yanzu ta ci wasa 13 da canjaras biyu jumulla.

Tun bayan da Real Madrid ta yi rashin nasara da ci 2-1 a gidan Real Betis ranar 8 ga watan Maris 2020, sai da kungiyar ta lashe wasa 10 a jere a La Liga daga lokacin.

Kuma a wasan na 10 a jere ta lashe kofin La Liga na bara, bayan da ta doke Villareal 2-1 ranar 16 ga watan Yuli ta kuma lashe kofin gasar na 34 jumulla.

Sannan ta buga canjaras a wasan karshe a kakar da aka karkare ta bara a gidan Leganes da ci 2-2.

Kakar bana kuwa ta 2020-21, Real ta fara da canjaras a gidan Sociedad, sai kuma ta lashe dukkan karawa uku da ta yi wato da Betis da Valladolid da kuma Levante..

Cikin wasan La Liga 15 a jere da ba a doke Real ba, masu tsaron bayanta sun taka rawar gani, inda mai tsaron raga Thibaut Coutois bai bar kwallo ta shiga ragarsa ba a wasa tara daga ciki.

Yayin da Madrid ta ci kwallo 27 a lokacin, Karim Benzema ne ya ci bakwai shi kuwa kyaftin Sergio Ramos yana da bakwai.

Real Madrid za ta kara da Cadiz ranar 17 ga watan Oktoba a gida a wasa na shida da za ta fafata a gasar La Liga ta shekarar nan, kuma Real Madrid tana ta daya a kan teburin bana.

Jerin wasannin da ba a yi nasara a kan Real ba a La Liga a 2019-20:

Ranar 8 ga Maris 2020

  • Real Betis2 - 1Real Madrid

Ranar 14 ga Yunin 2020

  • Real Madrid3 - 1Eibar

Ranar 18 ga Yunin 2020

  • Real Madrid3 - 0Valencia

Ranar 21 ga watan Yunin 2020

  • Sociedad1 - 2Real Madrid

Ranar 24 ga watan Yunin 2020

  • Real Madrid2 - 0Mallorca

Ranar 28 ga watan Yunin 2020

  • Espanyol 0 - 1Real Madrid

Ranar 2 ga watan Yulin 2020

  • Real Madrid1 - 0Getafe

Ranar 5 ga watan Yulin 2020

  • Ath Bilbao0 - 1Real Madrid

Ranar 10 ga watan Yulin 2020

  • Real Madrid2 - 0Alaves

Ranar 13 ga watan Yulin 2020

  • Granada1 - 2Real Madrid

Ranar 15 ga watan Yulin 2020

  • Real Madrid2 - 1Villarreal

Ranar 19 ga watan Yulin 2020

  • Leganes2 - 2Real Madrid

Kakar La Liga ta 2020-21

Ranar 20 ga watan Satumbar 2020

  • Sociedad0 - 0Real Madrid

Ranar 26 ga watan Satumbar 2020

  • Real Betis2 - 3Real Madrid

Ranar 30 ga watan Satumbar 2020

  • Real Madrid1 - 0Valladolid

Ranar 4 ga watan Oktoban 2020

  • Levante0 - 2Real Madrid