Man United: Telles da Diallo sun amince da taka leda a Old Trafford

Manchester United ta dauki dan kwallon tawagar Brazil, Alex Telles daga Porto da dan wasan Atalanta, Amad Diallo da zai koma Ingila a Janairu.

Telles ya saka hannu kan kwantiragin shekara hudu da yarjejeniyar tsawaita masa ita kaka daya.

Mai shekara 27 wanda ya buga wa kasarsa wasa daya, ya koma Old Trafford kan fam miliyan 13.6 da karin fam miliyan 1.8 kudin tsarabe-tsarabe.

United ta amince ta biya fam miliyan 19 kudin sayen Diallo da kuma karin fam miliyan 18.2 duk dai cikin cinikin.

Kungiyar da ke buga Premier ta ce matashin dan wasan zai koma ne da zarar ta kammala duba koshin lafiyarsa, idan ya kuma samu tazardar izinin taka leda a Ingila.

Shekara uku United ke bibiyar dan kwallon tun yana dan dagajinsa.

Dan kasar Ivory Coast ya ci kwallo a Serie A a wasan farko da ya buga a Oktoban 2019.

diallo bai buwa wa Atalanta wasa a bana ba, amma shi ne na biyu da aka haifa a 2002 da ya ci kwallo a daya daga manyan gasar Turai biyar watao Ingila da Faransa da Jamus da Italiya da Faransa, bayan matashin Barcelona Ansu Fati.