Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd 1-6 Tottenham: Tottenham ta ragargaji Man United
Tsohon koci, Jose Mourinho ya je ya caskara Manchester United da ci 6-1 a wasan da ya jagoranci Tottenham zuwa Old Trafford a gasar Premier League ranar Lahadi.
Son Heung-min da Harry Kane kowanne ya ci bibiyu, yayin da Tanguy Ndombele da kuma Serge Aurier kowanne ya ci guda-guda, a karawar da United ta kammala da 'yan wasa 10 a cikin fili.
Hakan na nufin ba wannan ne karon farko da aka ci United kwallo da yawa tun karbar aikin rikon kwarya da Ole Gunnar Solskjaer ya fara a Disambar 2018 ba, wannan shi ne kashin da kungiyar ta sha tun lokacin da babban jami'i mataimakin shugaba, Ed Woodward ya karbi aiki a 2013.
Da wannan sakamakon United ta koma ta 16 a kasan teburin Premier League na bana,
Tun fara wasan Tottenham ce ta mamaye karawar, ita ce kan gaba wajen rike kwallo tun kan a bai wa Anthony Martial jan kati, sakamakon yi wa Erik Lamela gula kan ramuwar marinsa a fuska da ya yi.
Tottenham ta koma ta biyar a kan teburin Premier League na bana, wacce ta buga wasa biyar cikin kwana 11 a gasa uku da ta fafatawa a shekarar nan, kuma ta yi nasara hudu da canjaras daya.
Manchester United za ta buga wasan gaba na Premier League a gidan Newcastle a St James' Park ranar 17 ga Oktoba.
Ita kuwa Tottenham tana da karawar hamayya ta birnin Landan da West Ham United a gida, kuma kwana daya tsakanin karawa da United za ta yi.
Tarihi mafi muni da ya faru kan United dangane da wasan
- Manchester United ta sha kashi a Premier League da kwallaye da yawa - da rashin nasara da kwallo biyar a karo na hudu a gasar kuma a karon farko tun cikin watan Oktoban 2011 da Manchester City.
- Tottenham ita ce ta farko da ta ziyarci United ta ci kwallo hudu tun kan hutu a Premier League tun bayan da ita ce dai ta yi nasara da ci 4-3 a Nuwambar 1957 da ta fara wannan bajintar.
- United ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere da ta buga a gida a bana kuma karo na biyar kenan a tarihin kungiyar na baya bayan nan shi ne kakar 1986/87 da aka doke ta karawa biyu a Old Trafford.
- Kocin Tottenham, José Mourinho ya yi kan-kan-kan da cin kwallo biyar a waje a Premier League a karon farko tun bayan bajintar da ya yi a Chelsea da ya doke Swansea City 5-0 a Janairun 2015.
- Manchester United ta karbi kwallo shida a raga a wasa daya a Premier League karo na uku kenan kuma kowanne a cikin watan Oktoba na farko a 1996 da Southampton, sai a 2011 da Man City,
- Wannan ne karon farko a Premier League da aka zura kwallo uku a raga a minti bakwai da take wasa tun bayan Burnley da Man City a Afirilun 2010,
- Dan kwallon Tottenham, Son Heung-Min da Harry Kane sune na farko da suka je Old Trafford suke da hannu a cin kwallo uku-uku a Premier League tun bayan Edin Dzeko a Oktoban 2011.
- Bruno Fernandes ya ci dukkan fenariti 10 da ya buga wa Manchester United a dukkan wasanni, wannan karon shi ne dai ya ci da wuri a Premier League (01:37) tun bayan ta Sergio Agüero da ya ci Newcastle a Fabrairun 2015 (01:12).