Real Madrid: 'Yan kwallo 11 ne suka ji rauni a bana

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mohammed Abdu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Ranar Juma'a 'yan kwallon Real Madrid biyu suka yi rauni da hakan ya sa Zinedine Zidane ya ajiye su karawa da Levante a gasar La Liga ranar Lahadi.
Tuni aka ce Dani Carvajal zai yi jinyar wata biyu, shi kuwa Alvaro Odriozola zai koma taka leada nan da mako biyu zuwa uku sakamakon raunin da suka yi.
Rashin Carvajal ko kuma Odriozola, ya kama dole Zidane ya nemi wanda zai maye gurbinsu tsakanin masu tsaron baya daga hagu da suka hada da Nacho ko Ferland Mendy ko kuma Lucas Vazquez.
Ƴan wasan da suka yi rauni a bana

Asalin hoton, Getty Images
Tun da aka fara wasannin atisaye don tunkarar kakar bana, 'yan wasan Real Madrid 11 ne suka ji rauni daban-daban, yayin da Hazard ya zama kan gaba wajen jinya tun zuwansa Real daga Chelsea.
Sauran da ke jinya sun hada da Marco Asensio da zai yi kwana 28 da Isco wanda zai yi jinyar kwana 18 sai Luka Jovic kwana tara da Lucas mai kwana 15.
Sauran sun hada da Marcelo kwana hudu da kuma Mariano Diaz.
Wanda suka fara jinya kwanan nan sun hada da Toni Kroos da kuma Eder Militao da Carvajal da kuma Odriozola har da dan wasan tawagar Belgium, Eden Hazard..
Wa zai maye gurbinsu?

Asalin hoton, Getty Images
A kakar bara da Odriozola da ya buga wasanni a Bayern Munich rabin kaka, Nacho ne ya yi jiran ko ta kwana ga Carvajal a Real Madrid.
Carvahal ya ci gaba da buga wasanni yadda ya kamata karkashin Zidane hakan ne ya sa Nacho ya ci gaba da dumama benci.
Nacho
Kamar dai Nacho, Lucas Vazquez ya ci gaba da taka rawar gani a karkashin jagorancin Zidane a Real Madrid.
Dan wasan ya yi fama da jinya da ta sa bai samu buga wasannin kamar yadda ya kamata ba, kuma hakan na da nasaba da raunin da ya dinga ji.
Zidane ya yi amfani da shi sosai a matakin mai tsaron baya daga hagu, kafin daga baya a auna kokarinsa wajen tare bayan Real Madrid.
A wasan daf da karshe a Champions League a kakar 2017-18 a karawa da Bayern Munich, Zidane ya yi amfani ne da Lucas wajen maye gurbin Carvajal.
Abinda Zidane ya yi a baya can

Asalin hoton, Getty Images
A karshen makon da za a karkare kakar bara, Zidane ya yi amfani da Ferland Mendy a matakin ko ta kwana wajen Carvajal mai tsaron baya daga gefen hagu.
Hakan ya biyo bayan da Mendy kan tsare baya daga gefen hagu a Lyon a lokacin da matsala ta taso, hasali ma yakan buga wurare da dama.
Kakar 2020-21
Kakar bana ta ci karo da koma bayan cutar korona, hakan ne ya sa Real Madrid ta tsuke bakin aljihunta domin ci gaba da wasannin shekarar nan ba tare da ta yi siyayya ba.
Annobar ta hana kungiyoyi su sayo fitattun 'yan kwallon da ake bukata, ganin cewar ana yin wasannin ne ba 'yan kallo, kuma ba karamar hasara ake tafkawa ba.
Wasannin da kungiya kan buga na da yawa idan ka hada da gasar La Liga da Copa del Rey ga Champions League ko Europa ga Nations Legue ga wasannin da 'yan wasan kan buga wa kasashensu.
Hakan na nufin dole ka samu 'yan kwallo masu nagarta da kwari idan har kana son kai wa ga nasara.
Sai kuma ga kakar bana ta zowa da Real Madrid da wani salo na 'yan kwallonta da ke zuwa jinya akai-akai.
Yanzu dai kakar bana aka farata, an kuma san lokacin da fitila kan haska ko kungiya za ta yi abin a zo a gani ko akasin hakan, kuma a watan Janairu za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai, kila lokacin Madrid ta dauko 'yan kwallo a wurin da take da matsala.
Wasu wasannin La Liga da Real Madrid za ta buga nan gaba:
Lahadi 18 ga Oktoban 2020
- Real Madrid da Cadiz
Lahadi 25 ga Oktobvan 2020
- Barcelona da Real Madrid
Lahadi 1 ga Nuwambar 2020
- Real Madrid da Huesca
Lahadi 8 ga Nuwambar 2020
- Valencia da Real Madrid
Lahadi 22 ga Nuwambar 2020
- Villarreal da Real Madrid
Lahadi 29 ga Nuwambar 2020
- Real Madrid da Alaves
Lahadi 6 ga Disambar 2020
- Sevilla da Real Madrid
Lahadi 13 ga Disambar 2020
- Real Madrid da Atl Madrid
Lahadi 20 ga Disambar 2020
- Eibar da Real Madrid











