Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Jorginho, Sessegnon, Walcott, Telles, Aouar, Hudson-Odoi, Alli

Arsenal za ta mayar da hankali wurin karbo aron dan wasan Chelsea da Italiya Jorginho, mai shekara 28, a yayin da fatanta na dauko dan wasanLyon da Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22, yake dusashewa. (ESPN)

Dan wasanTottenham Hotspur dan kasar Ingila da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Ryan Sessegnon, mai shekara 20, yana dab da tafiya kungiyar Hoffenheim da ke buga gasar Bundesliga. (Mail)

Newcastle United, West Ham United da kuma Crystal Palace sun bayyana aniyarsu ta karbar aron Theo Walcott daga Everton. (Teamtalk)

Manchester City za ta iya yin kafar-ungulu a shirin Manchester United na daukar dan wasan Porto Alex Telles inda ta soma zawarcin dan wasan na Brazil mai shekara 27. (90Min)

Chelsea ta yi watsi da tayin Bayern Munichna karbar aron dan wasan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 19, tare da zabin sayensa a kan £70m. (Mail).

Paris St-Germain tana shirin kara kudi domin dauko aron dan wasan Tottenham da Ingila Dele Alli, mai shekara 24, bayan an yi watsi da tayinta na farko. (Telegraph - subscription required)

Manchester United za ta fafata daLiverpool a yunkurin dauko dan wasan Barcelona dan kasar Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 23. (Sport - in Spanish)

AC Milan na son dauko dan wasan Chelsea da Jamus Antonio Rudiger domin ya yi zaman aro na kakar wasa daya, yayin da Tottenhamtake son daukar dan wasan. (Calcio Mercato - in Italian)

Juventus na tattaunawa da Everton domin sake daukar dan wasan Italiya Moise Kean, mai shekara 20, wanda ya bar kungiyar da ke buga gasar Serie A zuwa Toffees a 2019. (Corriere Dello Sport - in Italian)

Manchester United za ta bayar da £3.6m domin dauko dan wasa da ke buga gasar French Ligue 2 Sochaux dan shekara 16 Willy Kambwala. (RMC Sport via Sun)

Bayern Munich na dab da kulla yarjejeniyar £13.5m da Espanyol kan dan wasan Sufaniya Marc Roca, mai shekara 23. (Sport)

Paris St-Germain ta tuntubi Ajax domin tattaunawa kan dan wasan Argentina Lisandro Martinez, mai shekara 22. (AS - in Spanish)