Ross Barkley: Aston Villa ta dauki aron dan kwallon tawagar Ingila

Ross Barkley celebrates scoring for Chelsea against Barnsley in the Carabao Cup

Asalin hoton, Getty Images

Aston Villa ta kammala daukar aron dan kwallon tawagar Ingila, Ross Barkley daga Chelsea zuwa karshen kakar bana.

Barkley, wanda ya buga wa Ingila wasa 33, ya koma taka leda a Stamford Bridge daga Everton a Janairun 2018.

Mai shekara 26 ya buga wa Chelsea wasa uku a kakar bana ya kuma ci kwallo daya tal.

Barkley ya bar Everton wacce ya fara tun yana matashi, bayan da ya buga mata wasa 179 ya kuma ci kwallo 27.

Chelsea ba ta amfani da dan kwallon mai buga tsakiya, bayan da ta sayo Kai Havertz da Timo Werner da kuma Hakim Ziyech.

Kawo yanzu dan kwallon na Ingila bai buga wa Chelsea wasan Premier a kakar 2020-21 ba.

Sai dai ya ci kwallo a karawar da Chelsea ta doke Barnsley 6-0 a Caraboa Cup.

Barkley shi ne na biyar da Villa ta dauka a shekarar nan, bayan Bertrand Traore daga Lyon da Ollie Watkins daga Brentford da mai tsaron raga Emiliano Martinez daga Arsenal da kuma Matty Cash daga Nottingham Forest.