Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ruben Dias: Manchester City ta kammala daukar mai tsaron bayan Benfica
Manchester City ta kammala daukar mai tsaron baya Ruben Dias, mai shekara 23 daga Benfica kan yarjejeniyar shekara shida kan fam miliyan 65.
Dan wasan tawagar Argentina, Nicolas Otamendi ya koma Benfica daga City kan fam miliyan 13.7 a wani cinikin na da ban.
Dias ya zama dan kwallo na uku da kocin City, Pep Guardiola ya dauka a bana, bayan mai tsaron raga Nathan Ake da kuma Ferran Torres.
Dan kwallon tawagar Portugal, Dias ya fara buga tamauala daga karamar kungiyar Benfica daga baya ya koma babbar wacce ya yi wa wasa 113 ya kuma lashe kofin gasar Portugal a kakar 2018-19.
Ya kuma buga wa tawagar Portugal wasa 19, ana kuma sa ran zai dinke barakar bayan City waccce Leicester City ta zura mata kwallo biyar a gasar Premier League a karshen mako.