Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
William Troost-Ekong: Watford ta dauki dan wasan Najeriya daga Udinese
Watford ta kammala daukar dan kwallon tawagar Najeriya, mai tsaron baya, William Troost-Ekong daga Udinese kan yarjejeniyar shekara biyar.
An haifi dan wasan mai shekara 27 a Netherlands, wanda ya fara taka leda a matakin kwararre a kungiyar Groningen.
Ya koma Udinese a kakar 2018 kuma zuwansa Watford shi ne ciniki na kwanannan tsakanin kungiyoyin biyu wadanda iyalan Pozzo suka mallaka.
Haka kuma Watford ta kulla yarjejeniyar daukar matashi dan shekara 17, mai buga wa tawagar Guinea kwallo, Djibril Toure daga Ceffomig FC, kan kwantiragin shekara biyar da rabi.
Zai kammala komawa kungiyar daga ranar 1 ga watan Janairun 2021.