Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Lingard, Rice, Kounde, Mendy, Aouar, Ndombele, Suarez, Kean

Tottenham tana son dauko dan wasan tsakiyarManchester Uniteddan kasar IngilaJesse Lingard, mai shekara 27, a kan £30m. (Daily Star Sunday)

West Ham ta gaya wa Chelsea cewa ba za ta sayar da dan wasan Ingila mai shekara 21 Declan ba. (90min)

Sevillata ki amsa tayin da Manchester City a ta yi mata na sayen dan wasan Faransa mai shekara 21 Jules Kounde a kan euro 55m (£50.4m). (Marca)

Chelsea ta kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafar Faransa Rennes domin dauko golan Senegal Edouard Mendy, mai shekara 28, a kan £22m. (Observer)

Wolves na sha'awar dauko dan wasan Liverpool da Ingila mai shekara 27 Alex Oxlade-Chamberlain. (Sunday Mirror)

Leeds United za ta yi kokarin dauko dan wasan Manchester United Daniel James, mai shekara 22, idan Old Trafford ba ta bukatar dan wasan na Wales. (Daily Star Sunday)

Valencia na son kulla yarjejeniyar £6m don karbo golan Manchester United da Argentina Sergio Romero, mai shekara 33. (Sunday Mirror)

ShugabanLyon Jean-Michel Aulas ya ce ko dai Arsenal tana jan kafa ko kuma ba za ta iya biyan kudin da aka sanya kan dan wasan Faransa Houssem Aouar, mai shekara 22 ba. (Goal)

Ana hasashen cewa dan wasan Faransa Tanguy Ndombele, wanda aka rika rade radin cewa zai tafi Inter Milan ko Juventus, ya yanke shawarar zama a Tottenham bayan ya dinke barakar da ke tsakanisa da koci Jose Mourinho. (L'Equipe, via Football Italia)

KocinJuventus Andrea Pirlo ya ce "zai yi wahala" dan wasan Barcelona da Uruguay Luis Suarez, mai shekara 33, ya koma zakarun na Serie A. (Football Italia)

Kocin Barcelona Ronald Koeman ya bukaci dan wasan Sufaniya Riqui Puig, mai shekara 21, ya tafi zaman aro. (Marca)