Shin Chelsea na iya nuna aniyar lashe Premier a karawarta da Liverpool?

Wannan sharhi ne da matashi Abdulrazak Kumo ya rubuta inda ya yi nazari kan yadda Chelsea za ta iya budewa kanta kofar lashe gasar Firimiya ta bana idan har ta soma da kafar dama a karawar da za ta yi da Liverpool ranar Lahadi.

Abdulrazak Kumo dalibi ne a jami'ar Nile University da ke Abuja Najeriya, wanda ke matukar sha'awar kwallon kafa. Yanzu haka yana nan sashen Hausa na BBC domin sanin makamar aiki.

Chelsea mai zubin sabbin ƴan wasa za ta karɓi bakuncin Liverpool a Stamford Bridge a gasar Premier a ranar Lahadi yayin da manyan ƙungiyoyin na Ingila za su fara tantance makomarsu.

Chelsea za ta nemi wani matsayi na shiga sahun waɗanda za su iya lashe kofin gasar a bana idan har ta doke Liverpool.

Sabon zubin da Chelsea ta yi sun haɗa da Timo Werner da Kai Havertz and Thiago Silva, ko da yake Hakim Ziyech da Ben Chillwell suna jinya ba za su haska ba a karawa da Liverpool.

A ɗaya ɓangaren kuma, Liverpool ba ta da wani ƙalubale a tawagarta illa Oxlade Chamberlain da ya samu rauni yake jinya.

Chelsea ta fara da ƙafar dama inda ta doke Brighton ci 3-1 a wasan farko, yayin da kuma Liverpool da ke neman kare kofin Premier, ta sha da kyar ci 4-3 a karawar farko da Leeds.

A haɗuwar ƙungiyoyin biyu, za a farfado da hamayya ne tsakanin Lampard da Klopp. Ko Lampard ya shirya wa yaƙin lashe kofin Premier a bana? Ko Klopp zai ci gaba da abin da ya saba bayan doke Chelsea sau huɗu a jere.

Lahadi za ta tabbatar da haka.

Ina daraja Klopp - Lampard

Kafin haɗuwar Chelsea da Liverpool a ranar Lahadi, manajan Chelsea Frank Lampard ya ce yana matuƙar daraja Jurgen Klopp duk da tsamin dangantakar da ke tsakaninsa da kocin na Liverpool.

Lampard ya taɓa tayar da jijiyoyin wuya ga Klopp da kuma mataimakinsa Pep Lijnders a wasan da Chelsea ta sha kashi 5-3 a gidan Liverpool a bara. Ko da yake Chelsea ce ta kori Liverpool a gasar FA

Bayan wasan, Lampard da Klopp sun ta yin cacar baki tsakaninsu. Sake haɗuwarsu a ranar Lahadi ana ganin zai ja hankali.

A kakar da ta gabata tazarar maki 33 Liverpool da ta lashe kofin Premier ta ba Chelsea, amma ana ganin a bana irin kuɗaɗen da Lampard ya kashe ya yi zubin ƴan wasa, Chelsea za ta shiga sahun ƙungiyoyin da ake gani za su lashe kofin a bana.