Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Telles, Bale, Mendy, Dembele, Traore, Brewster
Manchester United ta kulla yarjejeniyar fatar baka da dan wasan Porto Alex Telles kuma dan kasar ta Brazil mai shekara 27 zai iya sanya hannu a kwangilar shekara biyar a Old Trafford. (RMC Sport - via Mirror)
Sai dai akwai bukatar United ta yi gaggawar dauko Telles idan ba haka ba Paris St-Germain za ta yi wuf da shi. (O Jogo - in Portuguese)
Hankalin wasu masu ruwa da tsaki a Real Madrid ya kwanta game da matakin da dan wasan Wales Gareth Bale ya dauka na son tafiya zaman aro a Tottenham. (AS - in Spanish)
Rennes tana son Chelsea ta sanya 'yan wasa biyu a duk wata yarjejniya da za su kulla ta dauko golan Senegal Edouard Mendy, mai shekara 28. Dan wasan Ingila Fikayo Tomori, mai shekara 22, na daya daga cikin 'yan wasan da kungiyar ta Faransa take so. (Football Insider)
Liverpool ta nemi karbo aron dan wasan Faransa da Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 23. (Sport)
Kocin Sheffield United Chris Wilder ya ce kungiyar ta tattauna da Liverpool kan karbo aron dan wasan Ingila Rhian Brewster, mai shekara 20. (Yorkshire Live)
Sai dai ita ma Crystal Palace tana son dauko Brewster. (90Min)
Manchester City na duba yiwuwar kulla yarjejeniay da dan wasan Sevilla dan kasar Faransa Jules Kounde, mai shekara 21. Hakan zai sa dan wasan Argentina Nicolas Otamendi, mai shekara 32, ya tafi Sevilla. (Telegraph)
Kocin Southampton Ralph Hasenhuttl ya ce babu wata maganar tattaunawa kan barin Danny Ings, mai shekara 28, kungiyar. (Daily Echo)
Har yanzu Leeds na son dauko dan wasan Argentina Rodrigo de Paul, mai shekara 26, daga Udinese. (Fabrizio Romano)