Paul Pogba: Ɗan wasan Manchester United ya koma atisaye amma da wahala ya buga wasansu da Crystal Palace

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manchester United ta sayi Paul Pogba a kan £89m

Mai yiwuwa Paul Pogba ba zai buga wasan farko na gasar Firimiya ta kakar bana da Manchester United za ta fafata da Crystal Palace ranar 19 ga watan Satumba ba.

Pogba bai buga wasan Nations League na Faransa makon jiya ba sakamakon kamuwa da cutar korona.

Kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya ce Pogba ya koma atisaye amma babu tabbacin za a saka shi a karawarsu da Palace.

Solskjaer ya shaida wa MUTV cewa: "Paul ba zai buga wasu wasanni ba saboda cutar korona."

"Ya yi gaggawar samun sauki kuma muna fatan zai buga wasan da za a yi a karshen makon gobe. Sai dai ba ni da tabbaci dari bisa dari."

Pogba bai buga galibin wasannin da kungiyar ta yi ba a kakar wasan da ta wuce saboda ya yi fama da rauni kodayake ya koma fagen tamaula lokacin da aka janye kullen cutar korona inda ya murza leda a kungiyar.