Paul Pogba ya murmure

Paul Pogba
Bayanan hoto, Paul Pogba ya shafe lokaci maitsawo yana jinya

Dan wasan tsakiyar Manchester United Paul Pogba zai dawo atisaye a wannan makon, kuma ya bayyana cewa a shirye yake ya hada kai da sabon dan wasan kungiyar Bruno Fernandes. (ESPN).

Paul Pogba ya shafe lokaci maitsawo yana jinya. (ESPN).

Mai tsaron bayan Everton Mason Holgate ya ce hankalinsa bai rabu ba, duk da rahotannin da ke cewa Manchester City na da sha'awar daukarsa.(Mail).

Mai horar da Chelsea Frank Lampard ya ce har yanzu mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga na da damar haskakawa a kungiyar nan gaba.(Mail).

Manchester United na ci gaba da zama kan gaba wurin ganin sun sayi dan wasan gaban Ingila da ke wasa a Borussia Dortmund na Jamus Jado Sancho.

Rahotanni sun ce United a shirye take ta sayi dan wasan kan kudin da ba'a taba sayen wani dan wasa ba a gasar Firimiya.(Telegraph).

Jaridar Express ta ruwaito cewa Liverpool da Manchester United sun shirya biyan fam miliyan 100.

Jadon Sancho
Bayanan hoto, Jadon Sancho

Kungiyoyin Real Madrid da PSG suma sun shiga jerin masu neman Sancho mai shekaru 19.(Mirror).

Hakama kungiyoyin na neman danwasan gaban RB Leipzig Timo Werner.(Express).

Arsenal na shirin taya mai tsaron bayan RB Leipzig Dayot Upamecano fam miliyan 50.(Express).

Mai horar da kulob din Crystal Palace Roy Hodgson ya shirya tattaunawa da mai kungiyar Steve Parish kan batun tsawaita kwantiraginsa.(Standard).

Mai tsaron ragar Manchester City Claudio Bravo na tunanin barin kungiyar zuwa kulob din New York City na Amurka. (Guardian).