Daniel Sturridge da Trabzonspor sun raba gari

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon dan wasan Liverpool, Daniel Sturridge da Trabzonspor sun raba gari bayan wata takwas a kungiyar.
Tsohon dan wasan tawagar Ingila ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku a kungiyar ta Turkiya.
Sturridge ya kuma buga tamaula a Manchester City da Chelsea da Bolton da kuma West Brom.
Dan kwallon ya lashe Champions League a Liverpool a bara, sannan ta soke kunshin yarjejeniyarsa.
Sturridge mai shekara 30 ya buga wasa 16 a kakar bana ya ci kwallo bakwai.







