Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Fraser, Sancho, Bale, Coutinho, Suarez, Dzeko
Dan wasan Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, ya amince ya tafi Newcastle bayan ya bar Bournemouth a bazara kuma ana shirin duba lafiyarsa ranar Litinin, a cewar jaridar Sky Sports.
Express ta ce kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya yi magana da dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, a kan komawa kungiyar daga Borussia Dortmund a bazarar nan.
Duk da burin Gareth Bale na barin Real Madrid, amma har yanzu kungiyar ba ta tayin daukar dan wasan na Wales ba, a yayin da dan kwallon mao shekara 31 ya ki yarda a rage albashinsa ko da za a samu kungiyar da ke kaunarsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Sabon kocin Barcelona Ronald Koeman ya gaya wa kungiyar cewa yana son Philippe Coutinho ya ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasan da muke ciki, maimakon a tura dan wasan na Brazil mai shekara 28 zaman aro a wata kungiyar. (Marca)
Dan wasan Barcelona Luis Suarez, mai shekara 33, zai yi jarrabawar koyon harshen Italiya ranar Litinin a yunkurinsa na neman takardar zama dan kasar, wacce za ta ba shi damar kammala tafiya Juventus.(Eurosport)
Dan wasan Bosnia Edin Dzeko, mai shekara 34, ya ce yana son barin Roma domin tafiya Juventus. (Corriere dello Sport - in Italian)
Barcelona na shirin yin tayin karshe kan dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23. (Goal)
Dole West Ham ta kusa ninka £27m idan tana son dauko dan wasan Burnley James Tarkowski, mai shekara 27. (Sun)
Tarkowski ya ce yana son buga Champions League "idan dama ta samu" kuma yana fatan shiga tawagar Ingila. (Telegraph)











