Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Thiago, Bale, Wijnaldum, Ampadu, Griezmann, Pogba

Thiago Alcantara

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara, mai shekara 29, ya yi watsi da rahotannin da ke alakanta shi da barin kungiyar, duk da rade radin da ake yi cewa dan wasan na Sufaniya zai tafi ko daiLiverpool ko kumaManchester United. (Manchester Evening News)

Har yanzu Real Madrid ba ta fid da tsammanin cewa dan wasanta mai shekara 31 dan kasar Wales Gareth Bale zai bar kungiyar a bazara ba. (Sport - in Spanish)

Manchester United, Arsenal da kuma Liverpool sun samu gayyatar dauko dan wasan Barcelona da Faransa wanda ya lashe Kofin Duniya Antoine Griezmann, mai shekara 29, bayan Lionel Messi ya yanke shawarar ci gaba da zama a Nou Camp. (Mail)

Liverpool ta shaida wa Barcelona cewa sai ta biya £15m idan tana son dauko dan wasan Netherlands Georginio Wijnaldum. (Mirror)

Kocin Wales Ryan Giggs ya yi amannar cewa dan wasa mai shekara 19 Ethan Ampadu zai fitar da gagarumar sanarwa kan makomarsa a Chelsea. (Sky Sports)

Newcastle sun nemi dauko dan wasan Bournemouth Callum Wilson a kan £20m sannan tana son kammala kulla yarjejeniya da dan wasan na Ingila mai shekara 28 kafin makon gobe inda za su fafata da West Ham a wasan farko na gasar Firimiya ta bana. (Sunderland Echo)

Dan wasanManchester United dan kasar Faransa Paul Pogba yana son komawa Juventus, kuma hakan ne ya sa bai sabunta kwangilarsa a Old Trafford ba a yayin da kwantaragin nasa za ta kare a 2021. (Tuttosport)

Golan United David de Gea ya wallafa hotonsa tare da dan kasarsa ta Sufaniya Sergio Reguilon a shafinsa na Instagram, lamarin da ya jawo ake rade radin cewa dan wasan na Real Madridmai shekara 23 zai tafi Old Trafford. (Manchester Evening News)

Tattaunawar da ake yi tsakanin Chelsea da Rennes kan golan Senegal Edouard Mendy, mai shekara 29, ta kai wani muhimmin mataki. (Sun)

'Yan wasanBarcelona Luis Suarez da Arturo Vidal, masu shekara 33, sun yi atisaye a wurare daban da na sauran 'yan wasan kungiyar ranar Asabar a yayin da dukkansu suke shirn barin kungiyar inda daya zai tafi Juventus yayin da dayan zai tafi Inter Milan. (ESPN)

Leeds Unitedna zawarcin dan wasan Barcelona dan kasar Brazil Rafinha, mai shekara 27. (Talksport)