Lionel Messi: Barcelona na son a biya ta Euro miliyan 700

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar gasar La Liga ta goyi bayan Barcelona a rikicinta da Messi da ke son raba gari da ƙugiyar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Lahadi ta ce kaftin ɗin na Barcelona da Argentina zai bar kulub din ne kawai idan an biya kudaɗen da aka amince a yarjejeniyarsa.
A makon da ya gabata ne Messi ya sanar da Barcelona kudirinsa na barin ƙungiyar da ya shafe ƙuriciyarsa yana taka wa leda, kuma ba kofin da bai lashe ba.
A Barcelona Messi ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan kwallon kafa na duniya sau shida, tarihin da babu wanda ya taɓa kafawa.
Messi ya bayyana aniyarsa ta raba gari da kungiyarsa ne bayan wulakancin ci 8-2 da Bayern Munich ta yi wa Barcelona kuma yana cikin fili a gasar zakarun Turai.
Barcelona ta shaida wa Messi cewa tana son ya ci gaba da taka leda a Nou Camp.
Messi ya nemi ya bar Barcelona ba tare da an biya kudi ba, kamar yadda yarjejeniyarsa ta bayyyana cewa zai iya barin kungiyar a karshen kakar 2019/20 a ƙashin kansa.
Sai dai Barcelona ta ce ƙarƙashin yarjejeniyar da ta amince da shi cewa za ta kare a ranar 10 ga watan Yuni kuma sai idan Messi ya kai wannan lokaci ne saboda tsawaita kakar wasanni da aka yi sakamakon annobar korona.
Ta ce ɗan wasan yana da lokaci har zuwa 31 ga watan Agusta domin yanke shawara. Ana ganin wannan zai iya kai su gaban kotu.
Messi ya ƙauracewa atisaye a ranar Lahadi, kuma bai je an yi masa gwajin korona ba na wasannan share fagen sabuwar kakar wasanni, wanda hakan na nuna yana son tilastawa Barcelona fitar da rai akansa.
Sanarwar da hukumar La Liga ta fitar ta bayyana matsayinta game da yarjejeniyar Messi a Barcelona.
Abin da sanarwar ta ƙunsa
Yarjejeniyar Messi ta bukaci ya kawo karshen yarjejeniyar kafin cikar wa'adinta, bisa kundin dokar Sarki ta 16 mai lambar 1006/1987 ta 26 ga watan Yunin 1985 ta alaƙar ma'aikata da waɗanda suka ɗauke su aiki kuma wadda ta shafi 'yan wasa.
Domin bin dokar da ke sasanta tsakani, da bin tsarin da ya kamata na kawo karshen wannan dambarwa, La Liga ba za ta bai wa Messi bizar da zai samu damar barin kasar ba har sai an biya kudaden yarjejeniyar.
Yarjejeniyar da Messi ya amince da Barcelona ta ƙarshe ƙungiyar ta bashi damar ya tafi duk lokacin da yake so, amma kuma duk wata ƙungiyar da ke buƙatarsa dole sai ta ajiye kudu yuro kusan miliyan 700.
Kuma Hukumar La Liga ba ta son Messi ya tafi ba tare da an biya kuɗin ba ga duk ƙungiyar da zai koma.

Asalin hoton, Getty Images
Abubuwa sun taɓarɓarewa Barcelona a gasar Zakarun Turai ta Champions League a shekara uku, kuma yanzu rikicin ya kara ta'azzara bayan burin dan wasan na Argentina na raba gari da ƙungiyar.
Rabon da Barcelona ta lashe gasar Zakarun Turai tun 2015, kuma yanzu kofin wannan gasar ne muradin Messi.
A bana an kammala kaka Barcelona ba ta lashe kofi ba inda Real Madrid ta lashe kofin La Liga duk da Barcelona ta lashe kofin a jere a kakannin da suka gabata.
Shekara uku a jere ana cin mutuncin Barcelona musamman rashin nasarar da ta yi a hannun AS Roma da (3-0) da Liverpool (4-0) sai a bana kuma inda Bayren Munich ta lallasa ta (8-2).
Akwai dai rikici tsakanin shugabannin Barcelona da kuma yan wasa da ake ganin ya jefa Barcelona cikin wannan halin.
Messi na cikin waɗanda suka caccaki daraktan wasanni na Barcelona Eric Abidal da kuma yadda ya zama ja gaba wajen rikici da shugaban kungiyar Josep Maria Bartomue.

Asalin hoton, Getty Images
Sabon kocin da Barcelona ta ɗauko Ronald Koeman ya buƙaci Luis Suarez babban abokin Messi ya tattara ya bar kungiyar.
Kwana guda bayan barazanar Koeman ga Suarez, Messi ya aike da wasikar barin Barcelona ranar Talata.











