Lionel Messi ya sake yi wa Barcelona tutsu, Everton na dab da dauko Rodriguez

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Manyan jami'a a Barcelona na sa ran cewa dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, zai tafi Manchester City, a cewar jaridar (Telegraph - subscription required)

Manchester City na fatan cin tudu biyu, inda za ta dauko Messi da kuma sabunta kwangilar kocinta Pep Guardiola. (Mirror)

Messi ya shaida wa Barcelona cewa ba zai je ta yi masa gwajin cutar korona ba ranar Lahadi. (Marca)

Mutumin da ya taimaka wa Messi zuwa Barcelona ya yi ikirarin cewa yana da tabbaci "kashi 90" cikin 100 cewa dan wasan zai ci gaba da zama a Nou Camp. (Manchester Evening News)

Everton za ta gwada lafiyar dan wasan Colombia James Rodriguez, mai shekara 29, a farkon makon gobe a yayin da take dab da kammala sayen dan wasan na Real Madrid. (Talksport)

Dan wasan Tottenham da Ivory Coast Serge Aurier, 27, ya ki amsa tayin tafiya Wolves a matsayin bangaren yarjejeniyar da za ta kai ga dan wasan Jamhuriyar Ireland Matt Doherty, mai shekara 28, ya tafi Tottenham. (Star)

Inter Milan ta gaya wa Tottenham cewa tana son daukar dan wasanta Tanguy Ndombele amma ta nemi ta rage farashin £55m da ta sanya kan dan wasan na Faransa mai shekara 23. (Express)

Dan wasan Ajax da Netherlands Donny van de Beek, mai shekara 23, yana jira ya gani ko Barcelona za ta yi zawarcinsa kafin ya yanke shawarar tafiya Manchester United ko Tottenham. (Sport)

An jinkirta shirin da Manchester City ta yi na sabunta kwangilar Kevin De Bruyne inda za ta rika ba shi £350,000 duk mako bayan jami'ai sun kama dan wasan na Belgium mai shekara 29. (Mirror)

Newcastle ce a kan gaba a yunkurin karbo aron dan wasan Arsenal dan kasar Ingila Rob Holding, mai shekara 24. (The Athletic - subscription required)

Newcastle ta nemi dauko dan wasan Arsenal Ainsley Maitland-Niles, mai shekara 23, sai dai ta ji haushi da aka sanya masa farashin £25m. Gunners sun ki karbar £15m daga wajen Wolves kan dan wasan a makon jiya. (Telegraph - subscription required)