Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Messi, Havertz, Thiago, Messi, Bergkamp, Gonzalez, Allan

Kai Havertz

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon mamallakin Inter Milan Massimo Moratti ya yi amannar cewa tsohuwar kungiyarsa tana son sayo dan wasan BarcelonadaArgentine Lionel Messi, mai shekara 33. (AS - in Spanish)

Chelsea na shirin kashe karin kudi fiye da yadda ta yi a baya bayan ta amince da yarjejeniyar dauko dan wasan Jamus mai shekara 21 Kai Havertz daga Bayer Leverkusen da kuma dan wasan Paris St-Germaindan kasarBrazil Thiago Silva, mai shekara 35. (The Times - subscription only)

Thiago ya ce zai yanke shawara kan makomarsa nan da awa 24 masu zuwa. (London Standard)

Koci Mikel Arteta yana son tsohon dan wasan Arsenal Dennis Bergkamp, mai shekara 51, ya koma kungiyar a matsayin mataimakinsa. (The Sun)

Daraktan wasanni na StuttgartSven Mislintat ya ce "da gaskeLeeds United take" wajen son dauko dan wasan Argentina Nicolas Gonzalez, mai shekara 22. (Yorkshire Evening Post)

Everton ta cimma matsaya da Napoli inda za ta biya £31.5m kan dan wasanta dan kasar Brazil mai shekara 29 Allan. (Daily Express)

Barcelona za takawo karshen kwangilar dan wasan Uruguay mai shekara 33 Luis Suarez. (RAC1 via Daily Mail)

Rundunar 'yan sandan Sweden ta gode wa dan wasan Manchester United Victor Lindelof, mai shekara 26, saboda kama barawon da ya yi wa wata tsohuwa fashi da makami. (Sky Sports)

Tattaunawar Wolves da Arsenal ta yi nisadomin kulla yarjejeniyar shekara hudu da dan wasanta mai shekara 22 dan kasar Ingila Ainsley Maitland-Niles. (Sky Sports).

Manchester United ta shirya tura golan Portugal Joel Pereira, mai shekara 24, domin zaman aro a Huddersfield Town on loan. (The Sun)

Valencia na son dauo dan wasan Real Madriddan kasar Sufaniya mai shekara23 Borja Mayoral. (Mundo Deportivo - in Spanish)