Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Magalhaes, Edouard, Brooks, Koeman, Messi

Asalin hoton, Getty Images
Aston Villa za ta biya £30m don dauko dan wasan Celtic dan kasar Faransa Odsonne Edouard, mai shekara 22. (The Scottish Sun)
Dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, ya amince ya tafi Arsenal kuma a makon gobe za a gama dauko shi a kan £27m. (The Guardian)
Bournemouth ba za ta yi kafar-ungulu ba game da duk dan wasanta da ke son barin - kuma hakan na nufin ta bai wa Manchester United damar dauko dan wasan Wales David Brooks, mai shekara 23. (Daily Mail)
Sabon kocin Barcelona Ronald Koeman yana son dauko dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 23, da dan wasan Manchester City dan kasar Sufaniya Eric Garcia, mai shekara 19, da kuma dan wasan Valencia dan kasar Sufaniya mai shekara 25 Jose Gaya. (Sport - in Spanish)
Kazalika Barca na zawarcin dan wasan Ajax dan kasar Argentina Nicolas Tagliafico, mai shekara 27. (Marca)
Haka kuma Koeman zai so dauko dan wasan Brazil Philippe Coutinho - dan wasan mai shekara 28 yana zaman aro a Bayern Munich a kakar wasa ta bana. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Mutumin da ke neman shugabancin Barcelona Jordi Farre ya ce an tattauna da kocin Liverpool Jurgen Klopp. (Sport - in Spanish)
Newcastle ta mika £4.5m ga kungiyar kwallon kafar Girka PAOK don dauko dan wasan kasar mai shekara 24 Dimitris Giannoulis. (Manu Lonjon via Sports Lens)
Kocin Arsenal Mikel Arteta yana so kocin Brentford da kuma kwararre kan wasan kwallon kafa Andreas Georgson su kasance cikin tawagarsa. (London Standard)
Luis Figo ba ya son dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, ya bi sahunsa ta hanyar barin Barcelona zuwa Real Madrid. (Marca)
Har yanzu dan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, bai sanya hannu kan sabuwar kwangila a AC Milan ba. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Dan wasan Juventus dan kasar Portugal Cristiano Ronaldo ne ya "ba da shawara" ga Manchester United ta dauko Bruno Fernandes, mai shekara 25, a cewar tsohon dan wasan United Patrice Evra. (The Guardian)











