Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hasashe kan 'yan wasa: Makomar Tagliafico, Traore, Sancho, Brooks, Magalhaes, Thiago, Havertz
Leicester City na son dauko dan wasan Ajax da Argentine mai shekara 27 Nicolas Tagliafico domin ya maye gurbin dan wasanta da ke shirin tafiya Chelsea Ben Chilwell, mai shekara 23. (Mail)
Wolves na shirin sayar da dan wasan Sufaniya Adama Traore, mai shekara 24, bayan an shaida wa kocinta Nuno Espirito Santo cewa dole ya samo kudin sayo 'yan wasa. (Mirror)
KazalikaWolves na son dauko dan wasan Sevilla mai shekara 26 dan kasar Argentina Lucas Ocampos domin maye gurbin Traore. (Sky Sports)
Manchester United ka iya janyewa daga tattaunawa da Borussia Dortmund a kan dauko dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, inda za ta koma kan batun nan da shekara daya. (Express)
BurinMan Utd na dauko dan wasan Wales David Brooks, mai shekara 23, ya samu tagomashi bayan Bournemouth ta amince cewa ba za ta yi kafar-ungulu kan dan wasan da ke son barin kungiyar ba. (Sun)
Arsenal tana kara samun kwarin gwiwa a kokarinta na sayen dan wasan Lille dan kasar Brazil Gabriel Magalhaes, mai shekara 22, amma Manchester United ta bukaci kungiyar da Gabriel ke yi wa tamaula ta jinkirta yanke hukunci. (Independent)
Kiran wayar da kocin Arsenal Mikel Arteta ya yi wa Magalhaes ne ya gamsar da dan wasan kan tafiya kungiyar. (Express)
Arsenal ta nemi dauko dan wasan Bayern Munich dan kasar Jamus mai shekara 29 Thiago Alcantara sai dai tana so Munich ta rage farashin dan wasan. (Mail)
*Aston Villa ta ware £30m don dauko dan wasan Celtic da Faransa mai buga gasar 'yan kasa da shekara 21 Odsonne Edouard, mai shekara 22. (Sun)
Daraktan wasanni naBayer Leverkusen Rudi Voller ya ce hankalin kungiyar ya kwanta a kan halin da dan wasanta mai shekara 21 dan kasar Jamus Kai Havertz yake ciki a yayin da Chelsea ke zawarcinsa. (Star)
Barcelona ta shirya ba da amsa ga dan wasan Argentina Lionel Messi, ko da dan wasan mai shekara 34 zai nemi barin kungiyar a wannan makon. (Mirror)
Arsenal da Barcelona na son dauko dan wasan Faransa mai shekara 21 Malang Sarr, wanda yake kasuwa bayan barin Nice. (Mail)