Champions League: Sabbin dokokin da aka sanya wa kungiyoyi takwas

Yan wasan Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Kokarin kungiyar Uefa na kammala gasar zakarun Turai wato Champions ya fuskanci koma-baya sakamakon annobar korona, wasannin kungiyoyi takwas da za a buga a gasar cikin kwanaki 12 a Lisbon.

Darajar kwallon kafa na cikin barazana, in ji hukumar kwallon kafa ta Turai, matukar ba abi ka'idojin da aka shimfida ba.

A Lisbon, duka kungiyoyin 8 din da suka yi saura da kuma masu gudanarwarsu, ciki har da wadda take buga Premier Ingila Manchester City za su tabbatar sun bi tsauraran dokokin da aka wallafa cikin shafi 31.

Wasu daga ciki za su bai wa manyan 'yan kwallo wuya.

Killace kai a otel

Bakin ruwa da sauran wurare a Lisbon za su kasance a rufe, yayin da za a iya barin 'yan kwallo su fita daga otel dinsu indan akwai wata yarjejeniya - kuma ba za su yi mu'amala da kowa ba idan suka fita bayan 'yan tawagarsu.

A kuma cikin otel, za a kyalesu su yi harkokinsu da juna cikin sirri, za a kebe wajen da suke cin abincin darensu, kuma masu aikin da ke cikin tawagarsu ne kawai za su iya kai musu abincin.

Kana bukatar a wanke dan kamfanka? Ma'aikatan tawagar ne kawai za su iya wanke kaya da sauran abubuwan amfanin 'yan kwallon.

Za a iya samun sauyi cikin mutum 11?

Rayuwar 'yan kwallo a wannan lokaci cike take da gwaje-gwajen cutar korona, kuma tsarin Champions ya sha ban-ban da ko wacce gasa.

Ana yin gwaji kan kulub ya tafi Portugal - mutum biyu sun kamu da cutar cikin tawagar Atletico Madrid kuma tuni aka cire su sakamakon hakan aka hana su yin tafiya.

Za kuma a karayin wani gwajin a Lisbon kwana guda gabanin wasa. Uefa ta yi alkawarin bayyana sakamakon gwajin sa'o'i shida gabanin take wasa.

Samun mutum guda ko biyu masu wannan cuta kan iya sauya tsarin da kungiyar ta yi game da wasanta.

Abin lura cikin ka'idojin da Uefa ta shifida shi ne, idan kungiya za ta iya samar da 'yan wasa 13 da kuma gola, to za a iya buga wasa. Amma in kungiyar ba za ta iya hakan ba, to za a iya basu damar sake dauko wasu 'yan wasan da ba a yi wa rijista ba.

Uefa na duba yiwuwar sake tsara wasanni ga ko wacce kungiya. Ka zalika ba za a sauya ranar da za a buga wasan karshe ba na gasar zakarun Turai daga 23 ga watan Agusta, maganar gaskiya ga duk kungiyar da ba za ta iya bin wannan tsari ba sai dai ta hakura da gasar.

Madubi a kofar bandaki

Idan gwajin da ake na cutar korna bai is aba, akwai Karin kwayoyin gwajin da za a iya tunani.

Jami'an lura kwayoyi masu kara kuzari za su ci gaba da sanya idanu kan samfurin fitsarin 'yan wasa.

Za a sanya madubi a wajen bandaki domin dokar ba da tazara, ta yadda jami'an za su rika sanya ido kan 'yan wasan.

Yin feshi ga ababan hawa da wajen fitar manyan baki

Dan wasan Manchester City Kyle Walker ya karbi jakarsa ne bayan ya sauka a Lisbon.

Dole ne a yi wa jirage da motoci feshi sosai, domin takaita haduwa da sauran mutane, kuma yan wasa za su rika bin wurin fitar manyan baki a tashohin jiragen sama.